An Ware Naira Biliyan 1.4 domin Saya wa Gwamna Ahmed Aliyu Sababbin Motocin Aiki

An Ware Naira Biliyan 1.4 domin Saya wa Gwamna Ahmed Aliyu Sababbin Motocin Aiki

  • Majalisar zartarwar jihar Sokoto ta amince da kashe sama da N5bn domin gyaran sansanin horar da matasa yan NYSC, sayen motoci da gina tituna
  • Gwamnatin ta ce kudaden za su taimaka wajen bunkasa ababen more rayuwa da inganta harkokin sufuri a jihar ta Sakkwato
  • Daga cikin abubuwan da za a yi akwai saya wa Gwamna Ahmed Aliyu motocin sulke domin ci gaba da jagorantar ayyukan gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Gwamnatin jihar Sakkwato ta amince da fitar da Naira biliyan 5 domin gudanar da wasu muhimman ayyukan more rayuwa.

Daga cikin ayyukan akwai gyaran sansanin masu yi wa kasa hidima na NYSC, sayen motocin gwamnati masu kariya daga harsashi da kuma gyaran hanyoyi a fadin jihar.

Gwamna Ahmed Aliyu.
Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu a taron majalisar zartarwa Hoto: Ahmed Aliyu
Source: Facebook

Gwamnatin ta amince da wadannan ayyuka ne a taron Majalisar zartarwa ta jihar Sakkwato da aka gudanar yau Laraba, 13 ga Mayu, 2026, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan

Bayan tadiye yaransa a tantancewar APC, Fubara ya magantu kan alakarsa da jam'iyya

Kwamishinonin filaye da gidaje, matasa da wasanni, kudi da sufuri, Barrista Nasiru Dantsoho, Injiniya Mustapha Kofar Marke, Injiniya Muhammadu Jabbi Shagari da Hon. Bala Kokani ne suka bayyana hakan bayan fitowa daga taron.

Za a gyara sansanin NYSC

Majalisar ta amince da kashe Naira biliyan 1.079 domin gudanar cikakken gyaran sansanin horas da masu yi wa kasa hidima na NYSC da ke jihar Sakkwato.

Haka kuma ta amince da kashe Naira biliyan 1.4 domin sayen motocin aiki a ofishin mai girma gwamna, ciki har da motocin Toyota Land Cruiser uku da harsashi ba ya fass su, Prado guda biyu da kuma motar bas kirar coaster.

Majalisar ta kuma amince da kashe Naira miliyan 438 domin sayen motocin bas guda shida don karfafa tsarin sufurin jama’a na jihar Sakkwato.

Sauran ayyukan da aka amince da su sun hada da kashe Naira miliyan 733.2 domin gyaran cibiyar taruka, yayin da aka ware Naira miliyan 340.5 domin sayen manyan motocin payloaders guda biyu ga ma’aikatar muhalli.

Za a gyara hanyoyi 36 a Sakkwato

A bangaren ababen more rayuwa, majalisar ta amince da kashe Naira biliyan 2.2 domin gyaran hanyoyi 36 a sassa daban-daban na jihar Sakkwato.

Kara karanta wannan

Hajjin 2026: Kasar Saudiyya ta yi gyare gyare, ta tura tallafi ga kasashen Musulmi 27

Hakazalika, aikin titin filin jirgin sama ya samu karin kudi har Naira miliyan 894.6 domin gaggauta kammala aiki,kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Sokoto.
Gwamna Ahmed Aliyu a fadar gwamnatinsa da ke cikin birnin Sakkwato Hoto: @ahmedaliyuskt
Source: Facebook

Majalisar ta kuma amince da kashe Naira miliyan 398.6 domin gina cibiyar kiwo da nufin bunkasa harkokin kiwo da sauran ayyukan tattalin arziki masu alaka da shi a jihar.

Kwamishinonin sun bayyana cewa dukkan wadannan ayyuka na daga cikin kokarin gwamnatin Sakkwato na inganta ababen more rayuwa, harkokin sufuri, da tsaftar muhalli.

An gano badakalar N117bn a Sakkwato

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Jihar Sokoto ta karɓi rahoton wani kwamitin bincike da ya zargi cewa an yi almundahanar fiye da Naira biliyan 117 a mulkin tsohon gwamna, Aminu Tambuwal.

An mika rahoton ne a hukumance ga Gwamna Ahmed Aliyu Sokoto a fadar gwamnati, lamarin da ya kara ce-ce-ku-ce a tsakanin mutanen Sakkwato.

Binciken ya gano manyan kura-kurai na kudi da suka haura ₦117bn, sakamakon rashin bin dokokin sayen kaya, raunin kulawa da kudi da kuma amfani da ikon gwamnati ba bisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262