Aliko Dangote Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Ya Fasa Sayan Kungiyar Arsenal

Aliko Dangote Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Ya Fasa Sayan Kungiyar Arsenal

  • Hamshakin attajirin da babu kamarsa a nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya yi tsokaci kan batun yunkurin sayan kungiyar Arsenal a shekarun baya
  • Aliko Dangote ya bayyana cewa wani lissafi ya yi a wancan lokacin, wanda hakan ya sanya ya yanke shawarar fasa mallakar kungiyar kwallon kafar
  • Hamshakin attajirin ya bayyana cewa ya auna ya ga abin da ya fi muhimmanci kan sayan kungiyar Arsenal da kuma kammala aikin matatar man sa da ke Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Shahararren mai kudin nan na Najeriya, Aliko Dangote, ya bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar janyewa daga babban burinsa na mallakar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.

Aliko Dangote ya ce ya gwammace ya mayar da hankali da kuma dukiyarsa wajen kammala matatar man fetur ta Dangote.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta kashe Dala biliyan 11.6 wajen biyan bashin kasashen ketare a 2026

Dangote ya yi maganar sayan kungiyar Arsenal
Aliko Dangote a wajen taron Africa Forward Summit a birnin Nairobi na Kenya Hoto: Ludovic Marin
Source: Getty Images

Jaridar Vanguard ta ce Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da shugaban hukumar gudanar da zuba jari ta bankin Norges, Nicolai Tangen.

Dangote ya kusa sayan kungiyar Arsenal

Dangote ya bayyana cewa ya kusa kulla yarjejeniyar a lokacin da darajar Arsenal take kusan Dala biliyan 2, amma daga karshe ya gane cewa zuba jari a aikin matatar man sa shi ne mafi alheri.

“Ni babban masoyin Arsenal ne, kwarai kuwa, na kusa siyan kungiyar. A lokacin da nake mayar da hankali kan siyan Arsenal, kuma ina kokarin ganin matatar man fetur tawa ta kammala."
"A wannan lokacin, darajar Arsenal takasance kusan Dala biliyan 2, sai na tambayi kaina: shin na saka Dala biliyan 2 na a Arsenal na bar kasuwancina ya lalace, ko kuma na ci gaba da kasuwancina sannan na ci gaba da kasancewa babban masoyin Arsenal.”

- Aliko Dangote

Dangote na goyon bayan Arsenal

Kara karanta wannan

An saki sunayen kananan hukumomi 3 da Boko Haram ta tilasta wa biyan haraji a Yobe

Dangote ya bayyana cewa ya zabi ya ci gaba da marawa kungiyar baya a matsayin masoyi maimakon ya mallake ta, The Punch ta kawo labarin.

“Saboda haka na yanke shawarar ci gaba da mara musu baya, ina kallon wasanninsu. Duk lokacin da Arsenal take wasa, nakan saka rigarsu. Ni masoyi ne, gara na ci gaba da kasancewa masoyi sannan na ci gaba da gudanar da kasuwancina."

- Aliko Dangote

Dangote ya ce ya fasa sayan kungiyar Arsenal
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote Hoto: Nur Photo
Source: Getty Images

Shin Dangote zai sayi Arsenal a yanzu?

Attajirin ya kara da cewa darajar kungiyar ta karu sosai tun daga wancan lokacin, wanda hakan ya sanya sayan ta a yanzu bai da amfani sosai.

“Kuma a yau darajarsu ta kai biliyoyin daloli, sayan ta bai dace ba kuma a yanzu."

- Aliko Dangote

Dangote zai zuba jari a harkar lantarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa hamshakin attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika, Aliko Dangote, ya bayyana cewa rukunin kamfaninsa na Dangote Group na shirin zuba jari a harkar samar da wutar lantarki.

Dangote na shirin samar da megawatt 20,000 na wutar lantarki, wanda ake ganin zai yaye duk wata matsalar karancin wuta a Najeriya.

Hamshakin attajirin ya kuma lissafo wasu manyan ayyukan da kamfaninsa ke yi, ciki har da samar da takin zamani, iskar gas (LNG), da gina tashar jirgin ruwa mai zurfi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng