Trump da Jinping Sun Cimma Matsaya kan Mashigar Hormuz da Iran Ta Kulle

Trump da Jinping Sun Cimma Matsaya kan Mashigar Hormuz da Iran Ta Kulle

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi wata ganawa da takwaransa na China, Xi Jinping a ranar Alhamis, 14 ga watan Mayun 2026
  • Fadar White House ta bayyana cewa shugabannin biyu sun tattauna batun mashigar ruwa ta Hormuz wadda Iran ta kulle tun bayan fara yaki
  • Ta bayyana cewa sun amince da cewa dole ne mashigar ta kasance a bude domin ci gaba da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin 'yanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Beijing, China - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, na ci gaba da ziyarar aiki da ya kai zuwa kasar China.

Fadar White House ta bayyana cewa, Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na kasar China, Xi Jinping, sun gudanar da wata "kyakkyawar" ganawa a ranar Alhamis, 14 ga watan Mayun 2026.

Trump ya tattauna da Xi Jinping na China
Xi Jinping na gaisawa da Donald Trump Hoto: Kenny Holston
Source: Getty Images

Fadar White House ta bayyana hakan ne a wani sako da ta sanya a shafinta na X a ranar Alhamis, 14 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Ana fargabar harin sojojin sama ya kashe kusan mutane 100 a Zamfara

Kasar Iran ta rufe mashigar Hormuz

Ta bayyana cewa shugabannin kasashen biyu sun amince cewa dole ne mashigar ruwa ta Hormuz "ta kasance a buɗe".

Iran ta kusan dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa gaba ɗaya ta wannan muhimmiyar hanyar ruwa, wadda kashi ɗaya bisa biyar na man fetur da iskar gas na duniya ke bi ta cikinta, tun bayan ɓallewar yaƙi da Amurka da Isra'ila a ranar 28 ga Fabrairun 2026.

Wace matsaya Trump da Jinping suka cimma?

"Bangarorin biyu sun amince cewa dole ne Mashigar Hormuz ta kasance a buɗe domin tallafawa zirga-zirgar makamashi cikin yanci."

Kasar China na fuskantar tasiri kai-tsaye sakamakon rashin man fetur ɗin da ke ratsawa ta mashigar Hormuz.

Tashar Channels tv ta ce a cewar kamfanin nazarin harkokin teku na Kpler, fiye da rabin danyen man da China ke shigo da shi ta teku yana fitowa ne daga Gabas Ta Tsakiya, kuma galibi yana ratsawa ta mashigar ne.

China za ta iya sayen man Amurka

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

A cewar fadar White House, Xi Jinping, ya nuna sha’awar sayen ƙarin man fetur na Amurka domin rage dogaron da kasar Sin ke yi da mashigar a nan gaba.

Sai dai rahoton da birnin Beijing ya fitar game da ganawar bai ambaci wata sha’awa makamanciyar wannan ba.

Trump ya gana da Xi Jinping
Shugaba Donald Trump tare da Xi Jinping a kasar China Hoto: @whitehouse
Source: Twitter

Amurka ta yi maganar batun Taiwan?

A nata ɓangaren, sanarwar fadar White House ba ta ambaci wata tattaunawa tsakanin shugabannin biyu kan batun Taiwan ba, tsibirin da ke mulkin kansa wanda Beijing ke ikirarin mallakarsa, kuma wani batu ne mai sarkakiya a diflomasiyyar Amurka da China.

Tun da farko, Xi Jinping ya yi gargaɗin cewa "rikici" tsakanin China da Amurka na iya ɓallewa idan har aka gudanar da batun ta hanyar da ba ta dace ba.

Amurka ta kashe kudade a yaki da Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Amurka ta bayyana makudan kudaden da ta lakume sakamakon yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Ma'aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ta sanar da cewa yaƙin da ƙasar ke fafatawa da Iran ya lakume fiye da dala biliyan 29 a cikin watanni biyu kacal.

Babban jami'in kuɗi na Pentagon, Jules Hurst III, shi ne ya tabbatar da sabon lissafin kudaden da Amurka ta kashe a yakin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng