Bayan Haduwa da Tinubu, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi Ya Gana da Wike

Bayan Haduwa da Tinubu, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi Ya Gana da Wike

  • Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya kai ziyarar girmamawa ga Khalifa Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi a gidansa da ke Asokoro, Abuja
  • Ziyarar ta kasance domin gaisuwa, nuna girmamawa da ƙarfafa dangantakar mutunta juna, yayin da suka tattauna batutuwan zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Najeriya
  • Ziyarar ta jawo ra'ayoyi daban-daban daga 'yan Najeriya, yayin da wasu ke ganin ta dace, wasu kuma ke kallonta da shakku saboda kusantar lokacin shirye-shiryen siyasar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya kai ziyarar girmamawa ga Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi a gidansa da ke Asokoro, Abuja.

An bayyana ziyarar a matsayin wata alama ta girmamawa da mutunta matsayin malamin, inda Wike ya kai masa ziyara domin gaisuwa da nuna ƙauna tare da ƙarfafa dangantakar mutunta juna.

Kara karanta wannan

An ware yanki 1 a Najeriya da ba za a kafa 'yan sandan jihohi ba

Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi da Nyesom Wike
Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi na magana da Nyesom Wike. Hoto: Khadimul Faidha Khalifatu Lisanul Faida Media
Source: Facebook

Shafin Khadimul Faida ya wallafa a Facebook cewa a yayin ziyarar, an tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.

Wike ya ziyarci malamin a gidansa

Rahoton ya ce Khalifa Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya karɓi baƙuncin Ministan FCT a gidansa da ke Asokoro.

A cewar rahoton, ziyarar ta kasance wata dama ta nuna girmamawa da ƙarfafa kyakkyawar dangantaka tsakanin mutanen biyu.

An kuma yi addu'ar Allah Ya ƙara wa Khalifa lafiya, tsawon rai da albarka, tare da ci gaba da ɗaukaka addinin Musulunci da shiryar da shugabannin Najeriya zuwa abin da zai amfani al'umma.

Me mutane ke fada?

Ziyarar Wike ga Khalifa Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ta jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan Najeriya, inda wasu suka bayyana cewa ziyarar ta dace, yayin da wasu ke ganin bai kamata a wannan lokaci ba.

Wasu daga cikin waɗanda suka yi tsokaci kan lamarin sun danganta ziyarar da yanayin siyasar Najeriya, musamman ganin yadda ake ƙara shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

An matsawa shugaban EFCC lamba ya sauka ko Tinubu ya kore shi

Nyesom Wike a wajen taro
Ministan Abuja, Nyesom Wike. Hoto: Lere Olayinka
Source: Twitter

Masu wannan ra'ayi na ganin cewa kusantar manyan malamai da shugabannin addini na iya zama wani ɓangare na ƙoƙarin neman goyon baya ko tasiri a siyasar shekarar 2027.

Sai dai har yanzu ba a bayyana cewa ziyarar tana da wata alaƙa kai tsaye da siyasar 2027 ba, kuma bayanin da aka bayar kan ziyarar ya fi mayar da hankali kan girmamawa, zaman lafiya da haɗin kai.

Khalifan Tijjaniyya ya gana da Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Babban Khalifan Ɗariƙar Tijjaniyya kuma shugaban Majalisar Ɗariƙar Tijjaniyya ta Duniya, Sheikh Sidi Ali Belarabi Tidjani, ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Abuja.

Sheikh Tidjani ya isa Najeriya ne ranar Alhamis, 6 ga Agusta 2026, tare da wata tawaga daga Khalifancin Ɗariƙar Tijjaniyya da ke Aïn Madhi a Algeria, biyo bayan gayyatar da wasu manyan shugabannin Tijjaniyya a Najeriya suka yi masa.

A yayin ganawarsu a fadar shugaban ƙasa ranar Juma'a, 7 ga Agusta, Sheikh Tidjani ya yi addu'ar samun zaman lafiya, haɗin kai, ƙauna da kwanciyar hankali a Najeriya, tare da bayyana fatan ƙara ƙarfafa dangantakar Algeria da Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng