Tsohon IGP, Usman Baba, Ya Janye daga Neman Takarar Gwamnan Yobe a APC, Ya Fadi Dalili

Tsohon IGP, Usman Baba, Ya Janye daga Neman Takarar Gwamnan Yobe a APC, Ya Fadi Dalili

  • Mutanen da ke neman takarar gwamnan jihar Yobe karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya sun rage yawa
  • Tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya sanar da janyewarsa daga neman takarar gwamnan Yobe a inuwar APC
  • Ya bayyana cewa matakin janyewar ya kasance mai wahala amma wanda ya zama dole domin samar da hadin kai da ci gaban jihar Yobe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Yobe - Tsohon shugaban rundunar ’yan sandan Najeriya (IGP), Usman Alkali Baba (mai ritaya), ya hakura da neman takarar gwamnan jihar Yobe a inuwar jam'iyyar APC.

Usman Alkali Baba ya janye daga neman takarar gwamnan jihar Yobe na zaben shekarar 2027 a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC.

Usman Alkali Baba ya janye daga takarar gwamnan Yobe
Tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba Hoto: AUB Support Group
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Usman Baba Alkali ya sanar da janyewar tasa ne a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Laraba, 13 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Ana fargabar harin sojojin sama ya kashe kusan mutane 100 a Zamfara

Meyasa tsohon IGP ya hakura?

Tsohon shugaban 'yan sandan ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki a harkar siyasa da abokan arziki a faɗin jihar da ma wajenta.

Hakazalika, ya ce ya ɗauki matakin ne domin muradin haɗin kan jam’iyya, zaman lafiya, da ci gaba gabanin zaɓen fitar da gwani na gwamna na jam’iyyar APC.

Usman Alkali Baba na son ci gaban Yobe

Usman Alkali Baba ya bayyana matakin a matsayin sadaukarwa mai wahala amma wadda ta zama dole domin haɗin kan jam’iyya mai mulki a jihar Yobe, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da hakan.

“Ba a cimma wannan matsaya cikin sauƙi ba; mataki ne na radin kai amma babban sadaukarwa ne da dole mu yi domin haɗin kan jam’iyya, zaman lafiya, da ci gaban jiharmu abin alfahari."

- Usman Alkali Baba

Usman ya ba magoya bayansa shawara

Ya buƙaci magoya bayansa da su kwantar da hankulansu, su ci gaba da marawa APC baya da kuma duk wanda ya fito a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni ya fadi matsayar APC kan zaben fitar da gwani a Yobe

“Bayan ɗaukar wannan mataki, muna kira ga dubun-dubatar magoya bayanmu da su nuna natsuwa, su kasance masu bin doka, kuma su ci gaba da marawa babbar jam’iyyar mu, APC, baya, gami da duk wanda zai zama ɗan takarar gwamna."

- Usman Alkali Baba

Usman Alkali Baba ya janye daga takarar gwamnan Yobe
Usman Alkali Baba tare da fom dinsa na neman tsayawa takara Hoto: AUB Support Group
Source: Facebook

Sauran mutum nawa ya rage?

Janyewarsa na zuwa ne ƙasa bayan da wani mai neman takarar gwamna a jam’iyyar APC, Alhaji Lawan Kolo Geidam, shi ma ya fita daga takarar.

Sauran masu neman takarar da suka rage sun haɗa da Sanata Ibrahim Muhammed Bomai, Mustapha Yunusa Maihaja, Bashir Sheriff Machina, da kuma Kashim Musa Tumsah.

'Yan takarar gwamnan Yobe sun gana da Shettima

A wani labarin kuma, kun ji cewa masu neman takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Yobe, sun gana da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Masu neman takarar sun ziyarci Shettima ne kan rikicin da ya dabaibaye batun magajin Gwamna Mai Mala Buni, wanda shi zai yi wa APC takarar gwamna a zaben 2027.

Rahotanni sun ce an gudanar da ganawar ne a gidan mataimakin shugaban kasa da ke Abuja cikin sirri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng