Shugaban China Ya Yi wa Trump Gargadi kan Taiwan da Suka Hadu a Beijing

Shugaban China Ya Yi wa Trump Gargadi kan Taiwan da Suka Hadu a Beijing

  • Shugaban China, Xi Jinping ya gargaɗi takwaransa na Amurka, Donald Trump, kan batun Taiwan a taron ƙasashen biyu da aka gudanar a Beijing
  • A bayanin da ya yi, Xi Jinping ya gargaɗi Donald Trump cewa idan ya yi wani kuskure game da Taiwan zai iya jefa ƙasashen biyu cikin babban rikici
  • Ya fadi haka ne yayin da suka gana a birnin Beijing ranar Alhamis, 14 ga watan Mayun 2026 a taron manyan ƙasashen biyu masu ƙarfi a duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

China - Donald Trump ya isa China yana yabon mai masaukinsa, inda ya kira Xi Jinping da “babban shugaba” kuma “aboki,” yana mai hasashen cewa ƙasashensu za su kyautata alaka.

Hakan na zuwa ne bayan shugaba Donald Trump ya fara wata ziyarar kwana biyu zuwa kasar China domin tattauna muhimman abubuwa.

Kara karanta wannan

Trump ya kama hanyar China, zai tattauna batun Iran da shugaba Jinping

Donald Trump da shugaban China Xi Jinping
Lokacin da shugaba Xi Jinping ya tarbi Donald Trump a China. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gargadin China ga Donald Trump

France 24 ta wallafa cewa duk da tarbar girmamawa da aka yi wa Trump, Xi ya yi magana cikin salo na dabam, inda ya ce ya kamata ƙasashen biyu su zama abokan hulɗa ba abokan hamayya ba.

Ya kuma jaddada batun Taiwan, wadda China ke kallon a matsayin wani ɓangare na ƙasarta duk da cewa tana cin gashin kanta, tun a farkon tattaunawar.

“Batun Taiwan shi ne mafi muhimmanci a dangantakar China da Amurka,”

In ji Xi, Kamar yadda the Guardian ta rahoto.

“Idan ba a tafiyar da shi yadda ya kamata ba, ƙasashen biyu za su iya faɗaawa a rikici, wanda zai jefa dangantakar China da Amurka cikin mummunan hali mai haɗari,”

Inji Xi yayin buɗe taron da ya ɗauki kusan sa'o'i biyu da minti 15.

Ziyarar Trump zuwa kasar China

Ziyarar Trump zuwa Beijing ita ce ta farko da wani shugaban Amurka ya kai China cikin kusan shekara 10, duk da cewa akwai rikice-rikicen kasuwanci da siyasa da ba a warware ba tsakanin ƙasashen biyu.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Tsuntsu ya firgita Trump a White House, ya dauka hari aka kawo masa

Xi ya tarbi Trump da jar dadduma a katafaren dakin taron Great Hall, inda aka yi kaɗe-kaɗen rundunar soja, harbe-harben girmamawa tare da tarbar yara 'yan makaranta suna tsalle suna cewa:

“Barka da zuwa!”

Trump, wanda ya nuna jin daɗinsa da wannan tarba, ya ce a yanzu dangantakar China da Amurka za ta fi kyau fiye da kowane lokaci da ya wuce.

Donald Trump da shugaba Xi Jinping
Shugaban Xi Jinping na gaisawa da Donald Trump a China. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Batun Taiwan dai ya daɗe yana zama babban ƙalubale tsakanin ƙasashen biyu, kuma an gagara kawo karshensa tsawon shekaru.

Amurka tana amincewa da gwamnatin Beijing a hukumance, amma dokokinta na cikin gida sun tilasta mata samar wa Taiwan makamai domin kare kanta.

Rasha ta kera babban makami

A wani labarin, kun ji cewa kasar Rasha ta kammala hada makamin Sarmat bayan shafe sama da shekara 20 tana kokarin hada shi.

Vladimir Putin ya bayyana cewa sun riga sun gwada makamin kuma zai iya kai wa yankunan duniya tare da keta kariyar sama ta Amurka.

Rasha ta gwada makamin ne a daidai lokacin da take cigaba da takun saka da Amurka da kasashen Turai, musamman kan Ukraine.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng