Manyan Labarai A Yau
'Yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da mataimakiyar shugaban karamar hukuma a jihar Ekiti. Daga baya jami'an tsaro sun samu nasarar ceto ta.
Hukumar kula da Alhazai ta kasa (NAHCON) ta kammala aikin jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki. An fara shirye-shiryen dawo da su gida Najeriya.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana mutanen da ke da hannu a matsalar rashin tsaro. Shugaban kasar ya ce suna yi masa fatan mutuwa.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi martani kan zargin yana yi wa Shugaba Bola Tinubu aiki don 2027.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wani matashi ya rasa rayuwarsa a rikicik da ya biyo bayan zaben fitar da gwanin APC a mazabar Sabon Gari da ke Kaduna.
Wani hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi magana kan batun yin takararsa a 2027. Ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar bai da shirin takara.
An yada wani bidiyo mai nuna cewa Farfesa Isa Ali Pantami yana sharbar kuka kan rasa tikitin jam'iyyar APC don takarar gwamnan jihar Gombe a zaben 2027.
Yayin da matatar Dangote ke shirye shiryen fara sayar da hannayen jari, shugaban kamfanin First HoldCo, Femi Otedola ya kai ziyara matatar da ke jihar Legas.
Babbar hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana nasarorin da aka samu kawo yanzu a hadin gwiwar sojojin kasar nan da na Amurka, yak ta'adda 175 sun tafi lahira.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari