Pantami Ya Sharbi Kuka kan Rasa Tikitin APC don Takarar Gwamna? An Gano Gaskiya

Pantami Ya Sharbi Kuka kan Rasa Tikitin APC don Takarar Gwamna? An Gano Gaskiya

  • Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya janye daga neman takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin inuwar jam'iyyar APC
  • An yada wani bidiyo wanda yake ikirarin cewa Farfesa Pantami ya sharbi kuka kan rasa tikitin APC don yin takarar gwamna
  • Bayan yada bidiyon, an gudanar da bincike domin gano ko na gaskiya ko kuma akasin abin da aka ce tsohon Ministan ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - An yada wani bidiyo wanda ke nuna tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami yana sharbar kuka.

A bidiyon an yi zargin cewa Farfesa Pantami na zubar da hawaye ne bayan hana shi tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027 na jihar Gombe.

An yada bidiyo kan Pantami
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami na jawabi a wajen taro Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Wani shafi mai suna daily_newspaper_headlines ne ya ɗora bidiyon a dandalin Tiktok tare da wani rubutu da ke cewa Pantami ya rushe da kuka bayan da aka hana shi tikitin na APC.

Kara karanta wannan

"Neman tutar APC aka daina": 'Dan Pantami ya ce takarar gwamnan Gombe na nan

An ce Pantami ya yi kuka

Rubutun na cewa:

“Tsohon Ministan sadarwa, Isa Ali Pantami ya jawo ce-ce-ku-ce na siyasa bayan da ya rushe da kuka biyo bayan cire shi da aka yi daga tsarin maslaha na takarar gwamna na APC a jihar Gombe."

Wani ɓangare na bidiyon ya nuna Pantami yana kuka tare da lasifika a gaba gare shi. Wani ɓangaren kuma ya nuna wasu maza biyu suna ɗaga hannun wani mutum daban sama domin nuna goyon baya.

Pantami ya nemi takarar gwamnan Gombe a APC

Tsohon ministan ya nemi takarar kujerar gwamnan Gombe a shekarar 2027. Ya kuma sayi fom ɗin tsayawa takara na APC domin kujera ta ɗaya a jihar Gombe.

Kwanan nan, ƙungiyar Pantamiyya Movement, wata ƙungiyar goyon baya mai biyayya ga Pantami, ta yi watsi da tsarin maslaha na APC a jihar don muƙaman zaɓe gabannin zaɓubbukan 2027.

Jam’iyyar APC a Gombe ta sanar da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takararta na maslaha na gwamna don zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu Alkali ya bi sahun Pantami, ya janye daga takarar gwamna a Gombe

Sai dai kuma, a ranar Talata, Pantami ya janye daga zaɓen fitar da gwani na takarar gwamnan Gombe na APC da aka tsara gudanarwa ranar 21 ga watan Mayun 2026.

An yi bincike kan bidiyon Pantami na kuka

Jaridar TheCable ta yi amfani da manhajar Google Lens domin bincikar hoton ɓangaren bidiyon da ke nuna Pantami yana kuka. Wannan bincike bai bayar da wani sakamako na gani da ido ba.

Bincike a shafukan sadarwa na Pantami ya nuna cewa yana ɗora bidiyon karatuttukansa na addini a dandalin YouTube.

An gano wani bidiyo na ƙasa da mintuna biyar, wanda aka wallafa ranar 1 ga watan Afrilu, 2024, inda aka hango Pantami yana kuka lokacin da yake wa’azi.

Hakazalika an lura cewa an haɗa taruka guda biyu daban-daban ne wuri guda domin su dace da iƙirarin da ake yi a bidiyon.

Pantami ya janye daga takarar gwamnan Gombe a APC
Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Twitter

Abin da bincike ya nuna

Hoton da ke ɓangaren hagu na bidiyon da ya bazu yana nuna amincewa da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takarar maslaha na gwamna na APC a Gombe ne da Inuwa Yahaya, gwamnan Gombe, da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka yi.

Kara karanta wannan

Pantami ya fusata, ya janye daga neman takarar gwamnan Gombe a APC, ya fadi dalili

Shi kuma bidiyon da ke ɓangaren dama, an ɗauko shi ne lokacin da Farfesa Pantami yake wa’azi.

Bidiyon da ke nuna Pantami yana kuka an ɗauke shi ne lokacin karatun addinin Musulunci a shekarar 2024, kuma ba shi da wata alaƙa da zargin hana shi tikitin takarar gwamna na Gombe.

Alkali ya ba Farfesa Pantami hakuri

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Alkali Salihu Zaria, ya yi magana kan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.

Malamin ya ba Pantami hakuri duba da irin yadda ake zargin an yi masa rashin adalci a zaben fitar da gwani na takarar gwamna a Gombe.

Sheikh Alkali Salihu ya ce tabbas Malam Pantami abin tausayi ne kuma ya cancanci a tausaya masa saboda dacin da ke cikin rasa mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng