Sojojin Amurka Sun Taimaka an Kashe 'Yan Ta'adda Sama da 100 a Najeriya
- Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce hadakar sojojin kasar nan da Amurka na ci gaba da haifar da sakamako mai kyau a yaki da ta'addanci
- Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Sama'ila Uba ya ce sojojin Amurka da na Najeirya sun halaka mayakan ISIS 175 zuwa yanzu
- Ya ce an an lalata wuraren binciken ‘yan ta’addan, ma’ajiyar makamai, cibiyoyin kayan aiki, kayan yaki da hanyoyin samun kudaden shiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta bayyana cewa an kashe mayaƙan kungiyar ta'addanci ta ISIS 175 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Ta bayyana cewa an murkushe wadannan yan ta'adda ne a hare-haren hadin gwiwa da sojojin Najeriya da na Amurka suka gudanar a wani bangare na yaki da ta'addanci.

Kara karanta wannan
Babban kwamanda da daruruwan yan ta'adda 175 da harin Amurka, Najeriya ya yi ajalinsu

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya fitar, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Ya ce an fara gudanar da hare-haren ne kwanaki kadan da suka gabata tare da hadin gwiwar rundunar sojojin Amurka mai kula da nahiyar Afirka watau AFRICOM.
An lalata sansanonin ‘yan ta’adda
Sanarwar ta ce zuwa ranar 19 ga Mayu, 2026, bayanan bincike sun nuna cewa an kashe mayaƙan ISIS 175 a hare-haren da sojojin suka kai a Arewa maso Gabashin Najeriya.
Ta kara da cewa an lalata wuraren binciken ‘yan ta’addan, ma’ajiyar makamai, cibiyoyin kayan aiki, kayan yaki da hanyoyin samun kudaden da suke amfani da su wajen kai hare-hare.
“Hadin gwiwar Najeriya da Amurka ta kuma yi sanadin kashe wasu manyan shugabannin ISIS, ciki har da Abu-Bilal al-Minuki, wanda ke daya daga cikin fitattun jagororin kungiyar a duniya,” in ji sanarwar.

Kara karanta wannan
Duk da ƙaryata Amurka, an tabbatar da hannun Trump a hallaka jagoran ISIS a Najeriya
An kashe manyan shugabannin ISWAP
DHQ ta ce Al-Minuki yana taka muhimmiyar rawa wajen tsara hare-haren kungiyar ISWAP, tara kudade, daukar mayaka da shirya kai hare-hare kan fararen hula a Najeriya da sauran sassan duniya.
A rahoton da The Nation ta wallaha, hedkwatar tsraon Najeriya ta kuma bayyana cewa mutuwarsa za ta kawo babban cikas ga tsarin jagoranci da ayyukan kungiyar.
Sauran manyan ‘yan ta’addan da aka kashe sun hada da Abd-al Wahhab, wani babban jagoran ISWAP mai kula da shirya hare-hare da yada farfaganda, da Abu Musa al-Mangawi.

Source: Twitter
Haka zalika, hedkwatar tsaro ta kara da sojojin Amurka da na Najeriya sun kashe Abu al-Muthanna al-Muhajir, wanda ke cikin masu samar da bidiyon yada farfagandar kungiyar.
Manjo Janar Uba ya ce wannan sabon aiki ya sake nuna kudurin rundunar sojin Najeriya na ci gaba da bibiyar ‘yan ta’adda da kuma kawar da su daga fadin kasar nan.
Tinubu ya yabawa sojojin Amurka
A wani rahoton, an ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da kashe babban kwamanda a kungiyar ISIS, Abu-Bilal Al-Manuki a yankin Tafkin Chadi.
Shugaban ya gode wa Amurka saboda haɗin gwiwar da take bayarwa wajen cimma manufofin tsaro na bai ɗaya, tare da nuna godiyarsa ga Shugaban Amurka Donald Trump.
A cewar shugaban ƙasar, rundunar sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar sojojin Amurka sun kai samamen cikin dare, inda suka kashe manyan yan ta'adda a Borno.
Asali: Legit.ng
