Gwamna Abba Ya Samu Shiga da APC Ta Zabi dan Takararta a Zaben Gwamnan Kano a 2027
- Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta bi tsarin maslaha domin zabar dan takararta na gwamna a zaben da za a gudanar a shekarar 2027
- APC ta zabi Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda zai yi mata takarar gwamnan jihar Kano a zaben da ake tunkara a badi
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna godiyarsa kan wannan amincewa da aka yi masa, ya yi alkawarin ci gaba da kawo romon dimokuradiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Jam’iyyar APC a jihar Kano ta zabi Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin ɗan takararta na maslaha domin zaben 2027 da ake tunkara.
Jam'iyyar APC ta zabi Alhaji Abba Kabir Yusuf ne a matsayin dan takarar gwamnan Kano gabanin babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce an gudanar da taron tabbatarwar ne a filin wasa na Sani Abacha Stadium da ke Kofar Mata a ranar Alhamis, 21 ga watan Mayun 2026.
Mutanen Kano sun yi cincirindo a taron APC
Taron ya shaida gagarumin fitowar magoya bayan jam’iyyar waɗanda suka bijire wa katsalandan ɗin mamakon ruwan sama domin su shaida wannan babban taro.
Daga cikin fitattun mutane da suka halarci taron tabbatarwar har da 'yan majalisa tare da manyan ma’aikatan gwamnati.
An ayyana Abba a matsayin dan takara
Shugaban kwamitin zaɓen fittar da gwani na Gwamna na APC, Muntari Shagari, ya ayyana cewa Abba Kabir Yusuf, an tabbatar da shi a matsayin ɗan takara tilo na zaɓen gwamnan Kano a shekarar 2027.
“A nan ina ayyana cewa Abba Kabir Yusuf, bayan ya gamsar da sharuɗɗan kundin tssarin mulki na APC, an tabbatar da shi a matsayin zaɓaɓɓen ɗan takarar gwamnan Kano na shekarar 2027."
- Muntari Shagari
Tun da farko, Sanata Barau Jibrin mai wakiltar shiyyar Sanatan Kano ta Arewa ya tura buƙatar ɗaukar Abba Kabir Yusuf a matsayin mai riƙe da tutar APC, yayin da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila na shiyyar Sanatan Kano ta Kudu ya goyi bayan buƙatar.

Kara karanta wannan
APC ta tabbatar da Dauda Lawal a matsayin 'dan takarar gwamnan Zamfara a zaben 2027
Gwamna Abba ya yi jawabi
A cikin jawabin karɓar takararsa, Gwamna Abba ya nuna godiyarsa ga dukkan wakilan saboda kishinsu da kuma sadaukarwarsu ga nasarar jam’iyyar a babban zaɓen 2027, jaridar Leadership ta kawo rahoton.
“A nan ina karɓar takara da tabbatarwar da wakilan APC suka yi mani na zaɓen gwamna a shekarar 2026."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf

Source: Facebook
Gwamnan, wanda ya yabi magoya bayan jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki saboda tabbatar da gudanar da aikin cikin zaman lafiya da nasara, ya yi alƙawarin samar da ƙarin romon dimokuraɗiyya idan har aka sake zaɓensa a wa wa’adi na biyu.
Gwamna Nasir ya zama dan takarar APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya samu tikitin jam'iyyar APC a zaben shekarar 2027.
Gwamna Nasir Idris, ya lashe tikitin takarar gwamna na APC na wa’adi na biyu, sakamakon samun amincewar wakilan jam'iyyar.
Nasir Idris ya samu nasarar ne bayan zama ɗan takara tilo na jam’iyyar ta hanyar amincewar bai-ɗaya daga wakilan dukkan mazaɓu 225 da ke faɗin jihar.
Asali: Legit.ng
