"Akwai Sauran Aiki": Shettima Ya Yi Gargadi kan Yaki da Ta'addanci

"Akwai Sauran Aiki": Shettima Ya Yi Gargadi kan Yaki da Ta'addanci

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi magana kan yakin da ake yi da kungiyoyin 'yan ta'adda da matsalar ta'addanci
  • Sanata Kashim Shettima ya yi gargadin cewa nasarorin da ake samu a 'yan kwanakin nan, ba su ke nuna yakin ya zo karshe ba
  • Mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa ba za a iya kawo karshen matsalar ta'addanci ta hanyar amfani da karfin soja kadai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya yi gargaɗi kan rikon sakainar kashi da matsalar rashin tsaro.

Shettima ya yi gargadin cewa, ko da yake an samu gagarumar nasara a yaƙi da ta’addanci, bai kamata a ɗauki waɗannan nasarori a matsayin cikakkiyar nasara ta ƙarshe ba.

Shettima ya yi gargadi kan rashin tsaro
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

Rahoton jaridar The Punch ya nuna cewa Shettima, wanda ya samu wakilcin Babban mataimaki na musamman kan ayyuka na musamman, Dr Aliyu Modibbo Umar, ya yi wannan tsokaci ne ranar Alhamis, 21 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Sojojin Amurka sun taimaka an kashe 'yan ta'adda sama da 100 a Najeriya

Me Kashim Shettima ya ce kan rashin tsaro?

Shettima ya yi magana ne yayin ƙaddamar da wani littafi mai suna ‘Counterterrorism and Counterinsurgency Operations in North East Nigeria’, wanda Manjo Janar Ibrahim Yusuf (mai ritaya) ya wallafa.

Ya ce ya kamata a kalli ƙalubalen tsaro na Najeriya a shekarun baya-bayan nan ba a matsayin shaidar raunin ƙasa ba, a’a, a matsayin jarrabawar juriya da ƙudurin al’ummarta, The Guardian ta dauko labarin.

“Abin da Najeriya ta jure a shekarun baya-bayan nan ba shaida ce ta ƙasar da haɗari ya mamaye ta ba, a'a, kyakkyawan hoto ne na juriya da jajircewar ’yan Najeriya waɗanda suka ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kare makomar da suka yi tarayya a kanta.”
"Yayin da aka samu gagarumar nasara wajen rage ƙarfin ’yan ta’adda, kada a ɗauki wannan ci gaba a matsayin nasara ta ƙarshe."
“Ta’addanci yana buƙatar dorewar sa ido, ci gaba da sauye-sauyen dabarun aiki, da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki."

Kara karanta wannan

Duk da ƙaryata Amurka, an tabbatar da hannun Trump a hallaka jagoran ISIS a Najeriya

- Kashim Shettima

Shettima ya ba da shawara

Shettima ya jaddada cewa ba za a iya doke ta’addanci da tarzoma ta hanyar amfani da matakan soja kaɗai ba, inda ya ƙara da cewa ana buƙatar cikakken tsari da ya haɗa da tattara bayanan sirri, fasaha, diflomaasiyya, sako al'umma, da kuma ci gaba domin samun zaman lafiya mai dorewa.

Ya yabi sadaukarwar da rundunar sojoji, hukumomin tattara bayanan sirri, ma’aikatan agaji, sarakunan gargajiya, shugabannin addini, da kuma ’yan ƙasa suke ci gaba da yi wajen daidaita yankunan da abin ya shafa a faɗin ƙasar.

Shettima ya yi gargadi kan rashin tsaro
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

An bukaci Tinubu ya sauke Shettima

A wani labarin kuma, kun ji cewa an yi kira ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya sauke mataimakinsa, Kashim Shettima a zaben 2027.

Wata kungiya ta magoya bayan gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ta roki Shugaba Tinubu da ya zabi gwamnan a matsayin abokin takararsa a zaben 2027.

Kungiyar ta bayyana cewa mambobinta a shirye suke su hada taron goyon baya daga tushe, ciki har da shirya gangamin mutane miliyan 10 domin goyon bayan tikitin Tinubu/Bala a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng