Gwamnan Kebbi Ya Samu Tikitin APC, Zai Nemi Wa'adi na 2 a Zaben 2027
- Jam'iyyar APC ta samu dan takarar da zai fafata a karkashin inuwarta a zaben gwamnan jihar Kebbi na shekarar 2027
- APC ta amince da Gwamna Nasir Idris a matsayin dan takararta domin ya nemi wa'adi na biyu a shekarar 2027 da ake tunkara
- Gwamna Nasir Idris ya nuna godiyarsa kan amincewar da aka nuna masa inda ya sha alwashin ci gaba da yin ayyuka a jihar Kebbi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC na wa’adi na biyu.
Gwamna Nasir Idris ya samu nasarar ne bayan zama ɗan takara tilo na jam’iyyar ta hanyar amincewar bai-ɗaya daga wakilan dukkan mazaɓu 225 da ke faɗin jihar.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce an gudanar da taron amincewa da gwannan ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Mayun 2026 a filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan
APC ta tabbatar da Dauda Lawal a matsayin 'dan takarar gwamnan Zamfara a zaben 2027
Gwamna Nasir ya samu goyon baya a Kebbi
Taron ya juye zuwa gagarumin nuna goyon baya ga gwamnan, wanda aka fi sani da “Kauran Gwandu,” yayin da magoya bayan jam’iyyar suka amince da dawowarsa domin zaɓen gwamna na shekarar 2027.
Shugaban kwamitin zaɓen fitar da gwani na gwamna na jam’iyyar APC, Abdulmalik Mahmud, ya ce kwamitin ya zo Kebbi ne kawai domin tabbatar da shawarar da mambobin jam’iyyar suka riga suka yanke a faɗin jihar.
“Aikinmu a nan yana da sauƙi ƙwarai domin mutanen Kebbi, musamman mambobin APC, sun riga sun yanke shawara."
- Abdulmalik Mahmud
Wakilan APC sun amince da Nasir Idris
Ya bayyana cewa kasancewar wakilai daga dukkan mazaɓu 225 wata alama ce mai ƙarfi ta haɗin kai da nuna kwarin gwiwa ga jagorancin gwamnan, jaridar Tribune ta kawo labarin.
“Bayan cika dukkan sharuɗɗan jam’iyyar da na doka, a nan ina ayyana Gwamna Nasir Idris a matsayin mai riƙe da tutar takarar gwamna na APC a Kebbi."

Kara karanta wannan
Gwamna Dikko Radda ya samu tikitin APC, zai nemi tazarce a zaben gwamnoni na 2027
- Abdulmalik Mahmud
Tun da farko, shugaban APC na jihar Kebbi, Abubakar Kana-Zuru, ya ce amincewar ta nuna shawarar gama-gari ta mambobin jam’iyyar domin ba gwamnan damar samun wa'adi na biyu.
“Dukkan mazaɓu 225 da ke Kebbi sun amince baki ɗaya su dawo da Kauran Gwandu a matsayin mai riƙe da tutar jam’iyyar. Shi ya sa muka taru a nan yau domin tabbatar da shi."
- Abubakar Kana-Zuru
Gwamna Idris ya nuna godiya
A cikin jawabin karɓar takararsa, Gwamna Idris ya siffanta wannan goyon baya a matsayin sabon umarni na nuna kwarin gwiwa daga al'umma, kuma ya yi alƙawarin ƙara kaimi ga ayyukan ci gaba a faɗin jihar.
“Ina farin ciki da cewa mutanenmu sun faɗi cewa sun amince da mu kuma suna son mu ci gaba. Wannan wata bayyananniyar alama ce da ke nuna kuna da gaskatawa ga jagorancinmu."
“Za mu yi duk abin da za mu iya domin samar da jagoranci mai inganci ga mutanen kirki na jihar Kebbi."

Kara karanta wannan
Ribas: Mutumin Wike na dab da zama 'dan takarar gwamnan APC bayan Fubara ya janye
- Gwamna Nasir Idris

Source: Facebook
Gwamnan ya kuma gode wa Shugaba Bola Tinubu, kwamitin gudanarwa na kasa na APC (NWC), da masu ruwa da tsaki a jihar saboda goyon baya da kwarin gwiwa da suka nuna ga gwamnatinsa.
Fubara ya janye daga neman takara a APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya hakura da neman takara a karkashin inuwar jam'iyyar APC.
Gwamna Siminalayi Fubara, ya janye daga shiga zaben fitar da dan takarar gwamnanAPC, wanda aka shirya gudanarwa.
Fubara ya ce bayan dogon tunani da tattaunawa da iyalansa, abokai da makusantansa, ya yanke shawarar janyewa daga neman takara domin amfanin jihar Rivers.
Asali: Legit.ng