Babbar Magana: 'Yan Bindiga Sun Sace Mataimakiyar Shugaban Karamar Hukuma
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi ta'asa a jihar Ekiti bayan da suka sace mataimakoyar shugaban karamar hukuma
- Tsagerun 'yan bindigan sun tasa keyar mataimakiyar shugaban karamar hukumar ne lokacin da takw tafiya a kan hanya
- Jami'an tsaro sun bazama aiki bayan samun labarin sace mataimakiyar shugaban karamar hukumar da 'yan bindiga suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ekiti - ’Yan bindiga sun yi garkuwa da Grace Ogunleye, mataimakiyar shugaban karamar hukumar Ilejemeje ta jihar Ekiti.
'Yan bindiga sun yi garkuwa ne da Grace Ogunleye lokacin da tafiya a kan hanyar Ipere zuwa Iludun a jihar Ekiti.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta ce majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba, 20 ga watan Mayun 2026, lokacin da take kan hanyarta ta dawowa daga wajen wani aiki.
'Yan bindiga sun yi aika-aika a Ekiti
Daga baya aka tsinci motarta a yashe a gefen hanya, lamarin da ya tada hankula game da inda take.
Yunƙurin tuntuɓar Ogunleye ta wayarta bai yi nasara ba, domin an bayyana cewa layin nata a kashe yake bayan faruwar lamarin.
An jiyo cewa Ogunleye ta ziyarci sakatariyar ƙaramar hukumar Ilejemeje da farko kafin ta nufi hanyar Ido Ekiti, inda maharan suka tare motarta suka yi awon gaba da ita.
Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, Falade Sunday, daraktan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na karamar Hukumar Ilejemeje, ya ce an sanar da hukumomin tsaro kuma ana ci gaba da ƙoƙarin ceto ta.
Sunday Abutu, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Ekiti, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.
Jami'an tsaro ceto wadda aka sace
Sai dai kuma, a cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar daga baya, rundunar ’yan sandan ta sanar da cewa an ceto Ogunleye lami-lafiya biyo bayan wani haɗin gwiwar ayyuka da ya haɗa da hukumomin tsaro daban-daban, jaridar Leadership ta kawo labarin.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun aikata ta'asa, sun sace shugaban makaranta da dalibai masu yawa a Oyo
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“An ceto wata da ake kira Mrs Ogunleye Grace, mataimakiyar shugaban karamar hukumar Ilejemeje, wadda ake zargin wasu miyagu da ba a tantance ba sun yi garkuwa da ita ranar 20 ga watan Mayu, 2026, lami-lafiya ba tare da wani rauni ba."
“Wannan gagarumar nasara ta zo ne sakamakon haɗin gwiwar ayyuka tsakanin ’yan sanda, sojoji, da sauran hukumomin tsaro gami da jami’an tsaron sa-kai, waɗanda suka duƙufa ga aikin ceto tare da matsa lamba ga miyagun.”

Source: Original
Sanarwar ta ce Falade Adegoroye Michael, kwamishinan ’yan sanda na jihar Ekiti, ya umarci da a gudanar da bincike na tsanaki kan lamarin.
'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Katsina da yankin Arewa maso Yamma.
Yan bindigan sun kashe aƙalla mutane 11, ciki har da jami'in tsaro da mace mai juna biyu, a harin sa suka kai hari kan wasu ƙauyuka biyu a karamar hukumar Bakori.
Harin ya faru ne da tsakar rana a ƙauyukan Gidan Wawu da Gidan Sarkin Noma, waɗanda maƙwabtan juna ne a karkashin gundumar Guga.
Asali: Legit.ng
