Hajjin 2026: An Bar Wasu a Najeriya yayin da NAHCON Ta Kammala Jigilar Maniyyata
- Hukumar kula da Alhazai ta kasa (NAHCON) ta kammala aikin jigilar maniyyata daga gida Najeriya zuwa kasa mai tsarki watau Saudiyya
- NAHCON ta bayyana cewa an kwashe maniyyatan na Najeriya ne zuwa kasar Saudiyya a cikin kwanaki 18, bayan fara jigilar a ranar, 3 ga watan Mayun 2026
- Hukumar NAHCON ta bayyana cewa wasu daga maniyyatan ba su samu damar zuwa Saudiyya ba saboda wasu dalilai da ba za a iya kauce masu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar kula da Alhazai ta kasa (NAHCON) ta kammala aikin kwashe maniyyatan Najeriya na shekarar 2026 zuwa kasar Saudiyya.
Wannan yana zuwa ne gabannin cikar wa’adin saukar jiragen saman aikin hajji a Masarautar Saudiyya kafin fara gudanar da rukunonin aikin hajjin.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar NAHCOM fitar ranar Alhamis, 21 ga watan Mayun 2026 a shafinta na X.
NAHCON ta kammala kwashe maniyyata
Hukumar NAHCON ta ce aikin jigilar, wanda aka fara ranar 3 ga watan Mayu, 2026, ya zo ƙarshe a hukumance tare da tashin jirgi na ƙarshe na kamfanin Max Air dauke da maniyyata daga jihar Zamfara, wanda ya tashi daga filin jirgin saman kasa da kasa na Gusau.
An gudanar da jimillar zirga-zirgar jiragen sama guda 98 a cikin kwanaki 18, inda aka riƙa yin kimanin jirage biyar a kowace rana.
An ware wa Najeriya jimillar gurbin aikin hajji na Alhazai 50,000 domin aikin na shekarar 2026. Wannan adadi ya haɗa da gurbi 9,750 da aka ware wa kamfanonin jiragen shakatawa masu lasisi, da kuma ma’aikata gami da jami’ai.
A daidai lokacin kammala jigilar, kusan maniyyata 30,000 daga cikin gurbin gwamnati, ban da jami'ai da wakilan gwamnati, aka yi nasarar kwashe su zuwa Masarautar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji.
Meyasa aka bar wasu maniyyata a Najeriya?
Sai dai kuma, wasu maniyyata ba su samu damar yin tafiyar ba saboda wasu yanayi da ba za a iya kauce masu ba, waɗanda suka haɗa da mutuwa da rashin lafiya bayan fitar da biza.

Source: Twitter
Hukumar ta bayyana cewa tana mika godiyarta ga Allah Maɗaukakin Sarki saboda tsari, zaman lafiya, da nasarar haɗin gwiwa tsakanin manyan masu ruwa da tsaki a duk tsawon aikin jigilar.
A halin da ake ciki, ana kammala shirye-shiryen ayyukan dawo da Alhazai gida Najeriya waɗanda aka tsara za a fara ranar 3 ga watan Juni, 2026.
Saudiyya ta gargadi mahajjata
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kula da yanayi ta kasar Saudiyya ta aika da sakon gargadi ga mahajjata kan karuwar yanayin zafi.
Hukumar ta gargadi mahajjata da su shirya wa matsanancin yanayin zafi, inda ake sa ran yanayin zafin zai tashi har zuwa digiri 47 na ma'aunin Celsius a lokacin gudanar da aikin hajjin.
Hakazalika, hukumar ta buƙaci mahajjata da su ɗauki matakan kariya domin kauce wa rukunonin cututtuka da zafi ke haifarwa.
Asali: Legit.ng

