Zaben 2027: Kwankwaso Ya Yi Martani kan Zargin Yana Yi Wa Tinubu Aiki

Zaben 2027: Kwankwaso Ya Yi Martani kan Zargin Yana Yi Wa Tinubu Aiki

  • Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano ya zargi madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da yi wa Shugaba Bola Tinubu aiki don zaben 2027
  • Kwankwaso ya fito ya yi martani kan zargin inda ya nuna cewa magana ce kawai ta teburin mai shayi wadda wawaye za su dauka
  • Tsohon dan takarar shugaban kasar a zaben 2023, ya nuna cewa da shi da Shugaba Bola Tinubu kowa ta kansa yake yi wajen neman mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan zargin yana yi wa Shugaba Bola Tinubu aiki don zaben badi.

Rabiu Kwankwaso ya yi watsi da iƙirarin da ke nuna cewa yana aiki ne domin muradin Shugaba Bola Tinubu gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

"Da izinin Kwankwaso," Wata sabuwa ta bullo kan yadda Gwamna Abba ya koma APC

Kwankwaso ya musanta yi wa Tinubu aiki
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a daren ranar Laraba, 20 ga watan Mayun 2026 a wata tattaunawa da kafar Global TV, wadda @Imranmuhdz ya sanya a shafinsa na X.

An zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki

Ya bayyana cewa wasu mutane sun daɗe suna yaɗa jita-jitar tun lokacin da yake a jam’iyyar New NNPP.

Sanusi Bature, mai magana da yawun gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi zargin cewa Kwankwaso, yana aiki ne a fakaice domin sake zaɓen Tinubu.

Ya yi zargin cewa Kwankwaso ya yi aiki ga Tinubu a shekarar 2023, kuma kwanan nan ya matsa lamba don samun ganawar kai-tsaye da shugaban ƙasar, wadda kuma ba ta tabbata ba.

Wane martani Kwankwaso ya yi?

Sai dai kuma, Kwankwaso ya ƙaryata waɗannan zargi, inda ya bayyana cewa wawayen mutane kawai za su yarda da waɗannan iƙirari.

“Ina jin wawayen mutane kawai za su yarda da hakan. Ba mu aiki ga kowa. Kawai muna aiki ne ga NDC."

Kara karanta wannan

Hadimin Gwamna Abba ya yi zargi kan Kwankwaso dangane da zaben 2027

“Bola Tinubu ya kasance babban ɗan uwana kuma aboki na gari har zuwa yanzu. Amma hakan ba yana nufin za mu haɗa dukkan dabarunmu na siyasa wuri guda da shi ba. Shi yana yin nasa, ni kuma ina yin nawa.”

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya ce ba a gayawa Tinubu gaskiya

Tsohon ministan tsaron ya ce ko da yake shi mamba ne na wata jam’iyyar siyasa ta daban, ya yi amanna cewa shugaban ƙasar bai san da matsalolin da ke addabar ƙasar ba saboda waɗanda ke kewaye da shi ba su gaya masa gaskiya.

Kwankwaso ya yi magana kan Tinubu
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jawabi a wajen taro Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook
“A al’adance a ƙarƙashin yanayin da ake ciki yanzu, shugaban ƙasar ba zai iya ganin abin da ke faruwa ba. Kuma abin takaici, mafi yawancin mutanen da ke kewaye da shi su ne ainihin suke haifar da matsalolin."
“Don haka, a irin waɗannan yanayi, yana da wuya a ga wanda zai ba shi shawara ko ya gaya masa ainihin halin da ake ciki. Abin da suka saba fada da abin da suke yi shi ne zaɓen gwamnoni. Ina jin idan aka duba adadin gwamnoni a yanzu, APC ce ta ɗaya.”

- Rabiu Musa Kwankwaso

Peter Obi ya gana da Kwankwaso

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana, za a ba shi tikitin takarar mataimakin shugaban kasa a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya ziyarci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

kai ziyarar ban-girma ga Rabiu Kwankwaso. Peter Obi ya ziyarci madugun na Kwankwasiyya ne kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 a daren ranar Talata, 19 ga watan Mayun 2026.

Jagororin biyu na NDC sun gana ne jim kaɗan bayan da kwamitin tantancewa na jam’iyyar ya tantance Obi domin takarar zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa gabannin babban zaɓen 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng