Attajirin Dan Kasuwa, Otedola Zai Zuba Jarin Dala Miliyan 100 a Matatar Dangote

Attajirin Dan Kasuwa, Otedola Zai Zuba Jarin Dala Miliyan 100 a Matatar Dangote

  • Shugaban kamfanin First HoldCo, Femi Otedola ya jagoranci tawaga sun kai ziyara matatar Dangote da ke jihar Legas yau Laraba
  • Yayin wannan ziyara, babban attajirin 'dan kasuwar ya bayyana shirinsa na zuba jarin Dala miliyan 100 a matatar man feturin
  • Hakan dai na cikin shirin tara Dala biliyan 2 da matatar Dangote ke nema daga masu zuba jari masu zaman kansu kafin kaddamar da tsarin IPO

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Attajirin 'dan kasuwar nan a Najeirya kuma shugaban kamfanin First HoldCo, Femi Otedola, ya bayyana cewa zai zuba jarin Dala miliyan 100 a matatar man Dangote.

Otedola ya sanar da shirin nasa ne ranar Laraba, 20 ga watan Mayu, 226 bayan ya jagoranci manyan jami’an kamfaninsa na First HoldCo sun kai ziyara matatar man Dangote da ke jihar Legas.

Kara karanta wannan

"Ku tashi tsaye ku kare kan ku daga ƴan bindiga," Hadimin Tinubu ga ƴan Najeriya

Femi Otedoila.
Shugaban kamfanin First HoldCo, Femi Otedola Hoto: @realFemiOtedola
Source: Getty Images

Otedola zai zuba jari a matatar Dangote

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa kudin da Otedola zai zuba na cikin shirin tara Dala biliyan 2 da matatar Dangote ke nema daga masu zuba jari masu zaman kansu kafin kaddamar da tsarin sayar da hannayen jari ga jama’a (IPO).

Idan baku manta ba a ranar 22 ga Oktoba, 2025, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewa matatar na iya sayar da kashi 10 cikin 100 na hannayen jarinta ga ya kasuwa.

Bincike ya nuna cewa kashi 5 cikin 100 na matatar Dangote na iya kai wa darajar kusan Dala biliyan 5.

Dangote na shirin sayar da hannun jari

Dangote ya kuma bayyana cewa matatar za ta bai wa yan Najeriya ciki har da talakawa damar zuba jari a cikinta, sai dai bai bayyana lokacin fara sayar da hannayen jarin ba.

Rahotanni sun ce Aliko Dangote na shirin yin tsarin IPO din ne a kasuwannin cikin gida da na kasa da kasa domin jawo hankalin masu zuba jari daga Afrika da sauran sassan duniya, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yadda aka ci zarafin Musulmi kan radin suna a Najeriya, kungiya ta yi korafi

Aliko Dangote.
Shugaban rukunin kammfaninin Dangote kuma attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka, Alhaji Aliko Dangote Hoto: Dangote Group
Source: Getty Images

A kwanakin baya, attajirin wanda ya zarce kowa tarin arziki a Afirka, ya bayyana cewa manufar IPO din ita ce bai wa ‘yan Afrika damar shiga cikin harkokin ci gaban masana’antu da kirkirar arziki a nahiyar.

Gabanin bude shirin zuba jarin, Otedola yakai ziyara matatar ta Dangote tare da tawagar kamfanin First HoldCo, inda ya ba da tabbacin cewa zai zuba akalla Dala miliyan 100.

Matatar Dangote ta rage farashin man jirgi

A wani rahoton na daban, an ji cewa matatar Dangote da ke jihar Legas ta rage farashin man jiragen sama na Jet A1 daga N1,750 zuwa N1,650 kan kowace lita.

Matatar hamshakin attajiri lamba daya a nahiyar Afirka ta ce ta yi haka ne domin rage wa kamfanonin jiragen sama nauyin kashe kudade tare da tabbatar da wadataccen mai a fadin kasa.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da kamfanonin jiragen sama da ke zirga zirga a cikin gida ke fama da tsadar gudanar da aiki, inda farashin man jiragen sama ke cin kaso mai yawa na kudaden su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262