Jonathan Zai Yi Takarar Shugaban Kasa a Inuwar PDP a 2027? Hadiminsa Ya Yi Bayani

Jonathan Zai Yi Takarar Shugaban Kasa a Inuwar PDP a 2027? Hadiminsa Ya Yi Bayani

  • Ana ta rade-radi dangane da batun yiwuwar takarar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, a zaben shekarar 2027
  • Wasu rahotanni sun nuna cewa tsohon shugaban kasar zai yi takarar kujera ta daya a Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyar PDP
  • Daya daga cikin hadimin Jonathan ya fito ya yi magana kan jita-jitar cewa ubangidan nasa zai zake neman takarar shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wani hadimi ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Wealth Dickson Omimim-Imagwa, ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa kan ubangidansa.

Hadimin na Jonathan ya yi watsi da jita-jitar da ke alaƙanta tsohon shugaban na Najeriya da tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP gabannin babban zaɓen 2027.

Hadimin Jonathan ya yi magana kan takarar ubangidansa a 2027
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan Hoto: @GEJonathan
Source: Facebook

Wealth Dickson Ominim-Imagwa ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 20 ga watan Mayun 2026 a wata tattaunawa da tashar News Central Tv.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar da gaske yake neman takarar shugaban kasa a zaben 2027

Me hadimin Jonathan ya ce kan takararsa?

Ya bayyana cewa babu wata shaida da ke nuna cewa tsohon shugaban ƙasar yana neman tsayawa takarar shugaban ƙasa ko kuma ya amshi wani tayin takarar shugaban ƙasa a cikin jam’iyyar PDP.

Imagwa ya mayar da martani ne ga iƙirari da jita-jitar siyasa na baya-bayan nan da ke nuna cewa ana duba yiwuwar bai wa Jonathan tikitin shugaban ƙasa na PDP gabanin babban zaɓen 2027.

A cewarsa, Jonathan bai bayyana sha’awarsa ga neman takarar shugaban ƙasa na 2027 ba, kuma bai ba wa wani mutum ko ƙungiya izinin sayen fom ɗin takara ko yin kamfen a madadinsa ba.

“Babu wata shaida a ko’ina da ke nuna cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yana takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027."

- Wealth Dickson Ominim-Imagwa

Ana yada jita-jita kan Jonathan?

Wannan ƙarin haske yana zuwa ne a tsakiyar sauye-sauyen siyasa da rahotanni dake zargin cewa wasu ’yan siyasa a cikin jam’iyyar hamayya suna yin ƙoƙarin lallaso Jonathan don ya shiga cikin tseren takarar.

Kara karanta wannan

"Ban nemi zama mataimakin Atiku ba": An fusata Rotimi Ameachi da tambayar tikitin ADC

A cikin makonnin baya-bayan nan, hotona da masu nuna goyon baya da ke da alaƙa da tsohon shugaban ƙasar sun bayyana a sassa daban-daban na ƙasar, lamarin da ya ƙara rura wutar jita-jita game da yiwuwar dawowarsa cikin harkokin siyasa gadan-gadan.

Jonathan ya musanta batun takara a 2027
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a wajen taron yaye dalibai Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Sai dai kuma, ɓangaren Jonathan ya sha nesanta tsohon shugaban ƙasar da irin waɗannan ayyukan, inda suka jaddada cewa ya ci gaba da mayar da hankali ne ga fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya, ginin zaman lafiya, da kuma ayyukan ƙasa da ƙasa.

Jonathan ya yi shugabancin Najeriya ne daga shekarar 2010 zuwa 2015 a ƙarƙashin inuwar PDP kafin ya rasa tazarcensa a hannun tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC a shekarar 2015.

Malami addini ya gargadi Jonathan

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani malamin addinin Kirista ya gargadi tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Primate Henry Chukwudum Ndukuba ya shaida wa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan da ya nesanta kansa da tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Malamin addinin Kiristancin ya buƙaci Jonathan da kada ya saurari kiran da ake masa na ya kasance a kan takardar zaɓe a shekara mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng