"Suna Mini Fatan Mutuwa"; Shugaba Tinubu Ya Fadi Masu Hannu a Matsalar Rashin Tsaro

"Suna Mini Fatan Mutuwa"; Shugaba Tinubu Ya Fadi Masu Hannu a Matsalar Rashin Tsaro

  • Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro wadda ta addabi sassa da dama na kasar mai arzikin man fetur
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa mutanen da ke da hannu wajen matsalar rashin tsaro na yi masa fatan mutuwa
  • Ya nuna cewa akwai mutanen da ya bakantawa rai sakamakon manufofin gwamnatinsa, inda suke son daukar ramuwar gayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan masu daukar nauyin matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Tinubu ya ce waɗanda suka amfana da zamanin tallafin man fetur mai cike da cin hanci da rashawa da kuma kasuwar musayar kuɗaɗen ƙasashen waje, su ne ke da alhakin ƙaruwar rashin tsaro a faɗin Najeriya.

Shugaba Tinubu ya yi magana kan rashin tsaro
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Tinubu ya yi magana ne ta bakin Olusegun Osoba, tsohon gwamnan Ogun, ranar Laraba, 20 ga watan Mayun 2026 a wajen taron ƙaddamar da wani littafi mai suna ‘The NADECO Story’, a Legas.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa

Tinubu ya fadi masu hannu a rashin tsaro

Shugaban ya ce wasu mutane marasa kishin ƙasa waɗanda suka duƙufa ga harkokin dabarun cin riba ta hanyar juya kuɗaɗen ƙasashen waje, suna adawa da sauye-sauyen gwamnatinsa, musamman janye tallafin man fetur da kuma haɗe kasuwannin musayar kuɗaɗe.

Tinubu ya ce waɗannan mutane masu son kai suna ƙoƙarin ruguza ƙasar ne a matsayin ramuwar gayya ga manufofin da suka kawo ƙarshen harkokinsu.

Osoba, wanda ya isar da saƙon shugaban ƙasar a cibiyar Muson Centre da ke Onikan a Legas, ya ce Tinubu ya sani sarai game da gangancin yunƙurin ruda zaman lafiyar ƙasa da mutanen da sauye-sauyen suka ɓata wa rai ke yi, jaridar TheCable ta kawo rahoton.

Tinubu ya ce ya kawo sauyi

“Ya san cewa akwai yunƙuri da gangan na ruda zaman lafiyar ƙasar nan da waɗanda ya sani ya ɓata wa rai ta hanyar soke tsarin farashin musayar kuɗaɗe daban-daban da kuma janye tallafin man fetur ke yi."

Kara karanta wannan

Babu imani: Wani ɗan masu kuɗi ya caccaka wa mahaifinsa wuka har lahira a Abuja

"Shugaban kasar ya bayyana tattalin arziƙi da tsaro a matsayin manyan batutuwan da suka mamaye hankalin gwamnatinsa a halin yanzu, kuma ya yi alƙawarin duba sauran batutuwan siyasa da suka rage bayan ya magance waɗannan manyan ƙalubale."
“Kuna iya ganin bambanci tsakanin kasuwar bayan fage da ta gwamnati kusan babu shi a yanzu. Naira, wadda ta kai kusan N2,000 akan dala ɗaya, yanzu tana kusa da N1,380."
“Waɗancan mutanen wadanda har yanzu suna ci gaba da juya kuɗaɗen, suna yi masa fatan mutuwa, amma ya ƙudurta cewa idan har wannan shi ne abu ɗaya tilo da zai yi domin sake fasalin tattalin arziƙi, a shirye yake ya fuskance shi.”

- Olusegun Osoba

Shugaba Tinubu ya fadi masu hannu a rashin tsaro
Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasar Najeriya Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Tinubu ya nada shugaban hukumar JAMB

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya nada sabon shugaba a hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB).

Mai girma Shugaba Tinubu ya nada Farfesa Segun Aina a matsayin sabon shugaban hukumar JAMB.

Farfesa Segun Aina, wanda zai cika shekaru 40 a watan Yulin 2026, zai maye gurbin Farfesa Is-haq Oloyede wanda wa’adinsa na biyu zai kare a ranar 31 ga watan Yulin 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng