Wata Sabuwa: Buba Galadima Ya Siffanta Bala Mohammed da Rabin Gwamna
- Jigon NDC, Buba Galadima, ya ce gwamnonin jihohi 34 da rabi suna goyon bayan ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027
- Galadima ya ce gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, bai yanke shawarar ɓangaren da zai mara wa baya ba tsakanin jam'iyyar gwamnati da 'yan adawa
- Ya kuma ce gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya nisanta kansa daga sansanin Tinubu, yana mai cewa Bala Mohammed ne ya zama “rabin” gwamna a yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jigon jam'iyyar NDC, Buba Galadima, ya yi ikirarin cewa gwamnonin jihohi 34 da rabi suna goyon bayan ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na sake neman wa'adi a zaɓen 2027.
Rahotanni sun nuna cewa Buba Galadima ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da kwamitin sulhu na ƙasa na jam'iyyar.

Source: Facebook
The Cable ta rahoto Buba Galadima ya ce gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, har yanzu bai yanke shawarar wanda zai mara wa baya ba tsakanin jam'iyyar mai mulki da 'yan adawa.
Maganar Galadima kan gwamnoni
Galadima ya ce gwamnan Oyo, Seyi Makinde, shi ne ɗaya daga cikin gwamnonin da ya bayyana cewa ba ya tare da Tinubu, kuma ba ya tare da NDC.
Ya ce saboda haka, daga cikin gwamnonin 36, Makinde shi ne wanda yake ganin a fili ya nisanta kansa daga sansanin Tinubu, yayin da Bala Mohammed yake matsayin “rabi” saboda bai fayyace matsayarsa ba.
“Gwamnoni 34 da rabi ne. Wanda ba ya tare da shi a fili shi ne Seyi Makinde. Rabin kuma shi ne Bala Mohammed,”
In ji Galadima.
Dalilin ambaton rabin gwamna
Buba Galadima ya ce Bala Mohammed ya gana da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki na NDC da misalin ƙarfe 3:00 na dare, inda suka rabu bayan tattaunawa kan makomar siyasa.
Sai dai ya ce da safe, gwamnan ya kira su ya sanar da cewa ya janye daga matsayar da ya ɗauka, bayan an ba shi shawarar kada ya shiga jam'iyyar da ke da ɗan takarar shugaban ƙasa mai ƙarfi.
A cewar Galadima, wannan ne ya sa yake ganin gwamnan Bauchi bai gama yanke shawarar ɓangaren da zai bi ba.

Source: Twitter
“Bala Mohammed yana tsakiya. Zai iya aiki tare da mu, ko kuma ya yi aiki tare da su. Shi ya sa a wurina rabi ne,”
In ji shi."
Gargadin Davido kan zaɓen Osun
A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen mawaki, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya ce zai nemi sa hannun Shugaban Amurka Donald Trump idan wani abu ya tafi ba daidai ba a zaɓen gwamnan jihar Osun.
Davido ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa kai tsaye da Carter Efe, inda ya bayyana sha'awarsa ga shiga siyasa da damuwarsa kan yadda ake gudanar da zaɓe a Najeriya.
Mawakin ya ce ba zai shiga siyasa ba har sai ya gamsu cewa tsarin zaɓen Najeriya yana da gaskiya kuma yana bai wa 'yan ƙasa damar zaɓar shugabanninsu cikin 'yanci.
Asali: Legit.ng

