APC Ta Tabbatar da Dauda Lawal a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Zamfara a Zaben 2027
- Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya lashe tikitin takarar gwamnan na APC ba tare da hamayya ba domin neman wa'adi na biyu a zaben 2027
- Mamobi da magoya bayan jam'iyyar APC daga mazabun jihar Zamfara sun tabbatar da Gwamna Lawal a matsayin 'dan takara ta tsarin masalaha
- Da yake jawabi godiya bayan tabbatar masa da takara, Dauda Lawal ya yi alkawarin ci gaba da ayyukan ci gaba idan jama'ar Zamfara suka sake ba shi dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Gwamna Dauda Lawal ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC domin neman wa'adi na biyu a zaɓen gwamnan jihar Zamfara na shekarar 2027.
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriyata tabbatar da Gwamna Dauda Lawal a matsayin dan takararta na gwamna ba tare da hamayya ba yau Alhamis, 21 ga watan Mayu, 2026.

Kara karanta wannan
Gwamna Dikko Radda ya samu tikitin APC, zai nemi tazarce a zaben gwamnoni na 2027

Source: Facebook
APC ta ba Gwamna Lawal takara
Gwamna Lawal ya samu tikitin ne ta hanyar tsarin maslaha da jam’iyyar APC ta amince da shi wajen gudanar da zaɓen fitar da gwani a jihar Zamfara, kamar yadda Channels tv ta rahoto
Magoya baya da mambobin jam’iyyar ta APC sun taru a mazaɓu daban-daban na jihar, inda suka amince baki ɗaya da Gwamna Lawal a matsayin ɗan takarar APC.
Yadda aka tabbatar da takarar Dauda Lawal
Sakamakon haka ne kwamitin zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC a Zamfara ya tabbatar wa gwamnan da nasara tare da mika masa tutar jam'iyya mai mulki.
Gwamna Dauda Lawal na cikin gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma bakwai da ke wa'adi na farko, wadanda za su nemi zarce wa zuwa wa'adi na biyu a babban zaben 2027 mai zuwa.
Gwamna Lawal ya gode wa jam’iyyar APC
Da yake magana da manema labarai bayan kammala taron, Gwamna Lawal ya gode wa mambobin jam’iyyar APC bisa amincewa da suka nuna masa a karo na biyu.

Kara karanta wannan
Ribas: Mutumin Wike na dab da zama 'dan takarar gwamnan APC bayan Fubara ya janye
Ya yi alƙawarin ci gaba da faɗaɗa ayyukan ci gaba da suka shafi inganta rayuwar al’ummar jihar Zamfara, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya nuna.

Source: Facebook
Ya kuma bukaci mambobin APC a lungu da sako na jihar au hada kai wuri guda domin nasarar jam'iyya a babban zaben da ke tafe.
Gwamna Dauda Lawal dai na cikin gwamnonin jam'iyyun adawa da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC bayan nasarar da suka samu a zaben 2023 da ya gabata.
Dikko Radda ya samu tikitin jam'iyyar APC
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta tabbatar da Dikko Umaru Radda a matsayin dan takararta na gwamnan jihar Katsina a babban zaben 2027 da ke tafe.
Da yake gabatar da gwamnan ga magoya bayan APC, shugaban kwamitin zaɓen fitar da gwani, Yakubu Machido, ya bayyana Radda a matsayin ɗan takarar APC ta hanyar maslaha.
Ya ce babu wanda ya fito neman takarar gwamnan Katsina a inuwar APC, don haka aka tabbatar da Malam Dikko Radda ba tare da hamayya ba.
Asali: Legit.ng