Malamin Addini Ya Hango Nasarar Peter Obi a 2027, Ya Kafa Masa Sharudda 3
- Wani fitaccen malamin addini na ƙasar Ghana ya yi hasashen cewa Peter Obi yana da gagarumar dama ta samun shugabancin Najeriya a shekarar 2027
- Prophet Clement Testimony ya bayyana sharuɗɗa guda uku da dole ne Obi ya cika su domin tabbatar da burinsa na zama shugaban ƙasa
- An ba Obi shawarar da ya ziyarci Shugaba John Dramani Mahama a ƙasar Ghana a matsayin wani ɓangare na cika burinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gabanin zaɓubbukan 2027, malamin addini na ƙasar Ghana, Prophet Clement Testimony, ya yi magana kan Peter Obi.
Prophet Clement Testimony ya bayyana cewa Peter Obi yana da gagarumar dama ta zama shugaban ƙasar Najeriya.

Source: Facebook
Prophet Clement Testimony ya yi wannan iƙirari ne kan Peter Obi a cikin wani bidiyo aka sanya a shafin Youtube.

Kara karanta wannan
Sanata zai rikita APC, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fitar da gwani a Cross River
Malamin ya taba yin hasashe kan Peter Obi
Idan za a iya tunawa cewa tun da fari mai wa’azin ya dauki hankalin jama'a ne sakamakon hasashen da ya yi gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a Najeriya.
A lokacin shekarar 2023, ya bayyana cewa Allah ya shirya wani “mutum mai tsaka-tsaki” domin ya ceci Najeriya, inda ya gano Obi, wanda a lokacin shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, a matsayin jagoran da Allah ya zaɓa.
Malamin addinin ya kuma yi iƙirarin cewa wasu dakaru za su yi ƙoƙarin hana Peter Obi nasara a rumfunan zaɓe.
Malamin addini ya hango nasarar Obi a 2027
A cikin wani sabon hasashensa, malamin ya ce:
“’Yan Najeriya, ku gaya wa Peter Obi cewa lokacinsa ya yi. Wannan mutumin shi ne David dinku, amma akwai abin da ya kamata a yi."
"Abubuwa guda uku da ya kamata ya yi domin ya zama shugaban ƙasar Najeriya. Ina da saƙo ga Najeriya; hasashen ya zo mini.”

Kara karanta wannan
Gowon ya fadi yadda Obasanjo ya bijire masa kan aiki ƙarƙashin Murtala a yaƙin Biyafara
“A wannan makon, ina yin addu'a. Ubangiji ya ce, ‘Gaya wa Peter Obi ya zo ya gan ka idan yana son ya zama shugaban ƙasar Najeriya.’ Yana buƙatar yin wasu gyare-gyare. Na gaya masa shekaru huɗu da suka gabata, ‘Rawanin naka ne, amma kujerar tana da nisa da kai."
- Prophet Clement Testimony
Malami ya ce lokacin Obi ya yi
Malamin ya ci gaba da cewa:
“Ina gaya muku, Najeriya, lokacin Peter Obi ya yi, amma na ajiye shi a cikin firiji. Ku gaya wa Peter Obi cewa lokacinsa ya yi.”
Yayin da yake bayyana cewa Obi, wanda babban jigo ne a jam'iyyar NDC, dole ne ya cika sharuɗɗa guda uku domin tabbatar da burinsa na shugaban ƙasa, Prophet Testimony ya ce zai bayyana guda ɗaya ne kawai a bainar jama'a.

Source: Facebook
A cewarsa, ya kamata Obi ya kai ziyarar ban-girma ga John Mahama a ƙasar Ghana.
“Idan ya zo, zan faɗi guda biyu da suka rage. Lamba ɗaya ita ce ya kamata ta zo Ghana. Ya kamata ya je ya haɗu da Shugaba John Mahama a wata ziyarar ban-girma."
"Zan gaya masa abin da ya kamata Shugaba Mahama ya yi masa. Lokacin da mutumin ya yi hakan, ƙofa ta farko ta buɗe wa Peter Obi.”

Kara karanta wannan
Duk da ƙaryata Amurka, an tabbatar da hannun Trump a hallaka jagoran ISIS a Najeriya
- Prophet Clement Testimony
Peter Obi ya magantu kan wa'adin da zai yi
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya yi magana kan wa'adin da yake son yi.
Peter Obi ya bayyana cewa wa’adi ɗaya na shekaru huɗu kadai zai yi idan aka zaɓe shi a shekarar 2027.
Obi, wanda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar NDC, ya yi ikirarin cewa ko da za a dora masa bindiga a tsakiyar kai, ba zai wuce zangon mulki daya a matsayin shugaban kasa ba.
Asali: Legit.ng