Manyan Labarai A Yau
Barrista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya ce shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa aikata laifuka da rikicin ƙungiyoyin daba a jihar.
Hukumar Federal Character Commission ta bayyana kura-kurai guda bakwai da ke hana masu neman aikin gwamnati samun nasara, tare da gargadin su guji masu damfara.
Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce za a ɗora wa Shugaba Bola Tinubu alhakin duk wani abu da ya samu Nasir El-Rufai, yana zargin an tsare shi ne saboda siyasa.
'Yan bindiga dauke da makamai sun farmaki wasu kauyukan jihar Benue. 'Yan bindigan sun hallaka mutane tare da raunata wasu da dama yayin harin da suka kai.
Halima Dangote ta bayyana cewa Aliko Dangote ya shirya bayar da kashi ɗaya bisa uku na dukiyarsa ga ayyukan alheri a matsayin wani ɓangare na shirin rabon gado.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai gana da Shugaban Amurka Donald Trump a Fadar White House domin tattauna yakin Iran da sauran batutuwan Gabas ta Tsakiya.
Kotun daukaka kara ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya umurci INEC ta soke rajistar ADC da wasu jam'iyyu hudu, tana mai cewa karar ba ta da inganci.
Sarkin Potiskum ya ce amfani da ƙarfin soja kaɗai ba zai kawo ƙarshen rashin tsaro a Najeriya ba, yana mai kira ga gwamnati ta magance talauci da rashin adalci.
Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto ta haramta wasu al’adun biki da suka haɗa da "Na Gani In So", kiɗan DJ da Wazigidi, tana mai cewa sun saɓa wa koyarwar Musulunci.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari