Dan Takara Ya Yi Alkawarin Samar da Lantarki a Kowane Gida cikin Watanni 11 a Najeriya
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP, Adewole Adebayo, ya yi alkawarin sanya tsarin solar mai ƙarfin kilowat 11 zuwa 15 a kowane gida
- Adebayo ya ce zai kafa masana’antun kera solar a faɗin Najeriya tare da horar da ’yan ƙasa kan girkawa da kuma kula da tsarin
- Ya kuma yi alkawarin ƙarfafa samar da wutar lantarki, tace ɗanyen mai a cikin gida da kuma yaƙi da satar ɗanyen mai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Adewole Adebayo, ya yi alkawarin samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin kilowat 11 zuwa 15 a rufin kowane gida.
Adebayo ya ce za a aiwatar da shirin cikin watanni 11 bayan ya hau mulki idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne ranar Talata, 8 ga watan Satumban 2026 yayin wata hira da shirin Prime Time na Arise Television, inda ya yi bayani kan manufofinsa na samar da wutar lantarki.
Ya yi alkawarin samar da solar ga gidaje
Adebayo ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen samar da makamashin hasken rana ga ’yan Najeriya, tare da rage matsalar ƙarancin wutar lantarki.
“Na yi alkawarin cewa za a sanya solar mai ƙarfin kilowat 11 zuwa 15 a rufin kowane gida cikin watanni 11,” in ji shi.
Ya ce gwamnatinsa za ta kafa masana’antun kera na’urorin solar a sassa daban-daban na Najeriya.
Haka kuma, zai samar da horo ga ’yan Najeriya domin su iya girka na’urorin da kuma gudanar da ayyukan gyara da kula da tsarin samar da wutar.
Ya ce ya riga ya gwada fasahar solar
Ɗan takarar SDP ya ce a baya ya taɓa ba gwamnati shawarwari kan matsalar wutar lantarki. Ya kuma bayyana cewa ya yi gwaji da fasahar solar a garinsu, inda ya ce ya horar da kusan mutane 2,000 kan yadda ake amfani da fasahar.
Adebayo ya ce shi da kansa yana kera wasu daga cikin na’urorin solar, ciki har da batirin lithium. Ya ce abin da bai samu damar kera shi da kansa ba shi ne inverter, don haka yana saye daga wasu masu samar da ita.
Ya ce za a kafa masana’antun solar
Adebayo ya ce Najeriya za ta iya haɗa gwiwa da ƙasashe kamar China, Turkiyya da Indiya domin kafa masana’antun kera solar a cikin ƙasar.
Ya ce ’yan Najeriya za su samu horo domin su iya gudanar da masana’antun da kuma kula da na’urorin.
A cewarsa, za a kafa wasu cibiyoyin samar da wutar solar da za su taimaka wa gidaje wajen gudanar da muhimman ayyuka tare da samar da guraben ayyukan yi.

Kara karanta wannan
Dan takarar shugaban kasa ya gano abin da ya hana a magance rashin tsaro a Najeriya

Source: Twitter
Adebayo ya hango faduwar Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ba wanda ba za a iya kayarwa ba ne a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Adebayo ya kuma yi hasashen cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta zo ta ƙarshe a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Asali: Legit.ng

