Zaben 2027: Kungiyar APC Ta Yi Barazanar Fallasa Sanata Ali Modu Sheriff
- Ƙungiyar Grassroots Movement for Tinubu Continuity Come 2027 ta nuna fargabar yiwuwar Ali Modu Sheriff ya aikata abin da zai saba wa APC a 2027
- Sani Ahmad Zangina ya ce ya kamata shugabancin APC ya sanya ido kan ayyukan manyan ’ya’yan jam’iyyar gabanin babban zaɓen 2027
- Ƙungiyar ta nuna shakku kan wasu abubuwa da da ta ce tsohon gwamnan na Borno ya aikata a lokacin zaben 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ƙungiyar Grassroots Movement for Tinubu Continuity Come 2027, wadda ke yaƙin neman sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta nuna fargabar yiwuwar cin dunduniyar APC a zaben 2027.
Ƙungiyar ta danganta damuwar da tsohon gwamnan jihar Borno kuma Sanata, Ali Modu Sheriff, gabanin babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
Ƙungiyar ta yi magana kan Ali Modu Sheriff
Jaridar Daily Trust ta ce shugaban kungiyar na ƙasa, Kwamares Sani Ahmad Zangina, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi.
Zangina ya yi magana ne kan sauye-sauyen siyasa da ake samu gabanin zaɓen 2027 da kuma yadda abubuwa ke gudana a cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Ya yi zargin cewa damuwarsa ta samo asali ne daga abin da ya bayyana a matsayin salon siyasar da Sheriff ya taɓa nunawa a baya, musamman a lokacin babban zaɓen 2023.
An tuna da zaɓen 2023
A cewar Zangina, irin wannan damuwa ta taso a lokacin zaɓen 2023, inda aka yi zargin cewa akwai wasu batutuwa da suka shafi Sheriff da tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu.
Sai dai Zangina bai gabatar da wata sabuwar hujja da za ta tabbatar da cewa Ali Modu Sheriff na da wani shiri na cin dunduniyar jam’iyyar a zaɓen 2027 ba.
Ya buƙaci shugabannin APC da su sanya ido sosai kan ayyukan manyan ’ya’yan jam’iyyar yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
An buƙaci a bi kundin tsarin APC

Kara karanta wannan
Duk da shirin haɗakar yan adawa, Jigon PDP ya sallama wa Shugaba Tinubu a zaben 2027
Zangina ya kuma yi kira ga shugabancin APC da ya tabbatar da cewa dukkan manyan ’ya’yan jam’iyyar suna bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar, umarninta da kuma dokokin zaɓe da suka dace.
Ya ce ya kamata a samar da hanyoyin da za su ba jam’iyyar damar bincike da magance duk wani sahihin zargi na ayyukan da za su saba wa jam’iyya.
A cewarsa, bai kamata a bar wani mutum ya lalata muradun jam’iyyar baki ɗaya ba saboda matsayinsa ko irin tasirinsa a cikin siyasa.
An ce manufar ita ce kare APC da Tinubu
Zangina ya bayyana cewa matsayin ƙungiyar ba wai an ɗauke shi ne domin kai hari ga wani mutum ba, illa dai domin kare haɗin kan APC da kuma damar Shugaba Tinubu ta samun nasara a zaɓen 2027.
Ya ce ƙungiyar na son ganin an samu daidaito da bin ƙa’idojin jam’iyya domin kauce wa duk wani abu da zai iya kawo cikas ga shirinta na tunkarar babban zaɓen ƙasar.

Source: Facebook
Ba a tabbatar da zargin ba
Duk da zargin da ƙungiyar ta yi, babu wata hujja da aka gabatar da ta tabbatar da cewa Sanata Ali Modu Sheriff yana da wani shiri na cin dunduniyar APC a zaɓen 2027.
Saboda haka, zargin da ƙungiyar ta gabatar ya kasance zargi ne kawai, kuma ba ya tabbatar da aikata wani laifi ko shirin cin amanar jam’iyya.
Ali Modu Sheriff ya magantu kan Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Ali Modu Sheriff, ya yi watsi da damar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Sanata Ali Modu Sheriff ya jaddada cewa yanzu ba lokacin Arewa ba ne na fitar da shugaban kasa na gaba a Najeriya.
Asali: Legit.ng

