'Yan Takarar Gwamna na ADC a Jihohin Arewa Sun Dauki Muhimman Alkawura

'Yan Takarar Gwamna na ADC a Jihohin Arewa Sun Dauki Muhimman Alkawura

  • Yan takarar ADC na gwamna a jihohin Arewa maso Yamma bakwai sun rattaba hannu kan yarjejeniya gabanin zaɓen 2027
  • Abubakar Malami ya ce ’yan takarar sun amince da aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N110,000 ga ma’aikata a jihohin yankin
  • ’Yan takarar sun zargi gwamnonin APC da gaza magance matsalar tsaro, talauci da rashin ingantattun ayyukan more rayuwa a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gabanin babban zaɓen 2027, ’yan takarar kujerar gwamna na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihohin Arewa maso Yamma bakwai sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo ci gaba.

An yi wa yarjejeniyar taken “Northwest ADC Governorship Candidates’ Compact 2027–2031”, inda aka mayar da hankali kan kare ’yan ƙasa, yin gyare-gyare da kuma kula da albarkatun gwamnati yadda ya kamata.

Yan takarar gwamna na ADC sun yi alkawura
'Yan takara gwamna na ADC a jihohin Arewa maso Yamma Hoto: Walin Sokoto Media Team
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce tsohon Antoni-Janar na Tarayya, Abubakar Malami, ya yi magana a madadin ’yan takarar.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa ya tafi hutu, zai yi gagarumin shiri don zaben 2027

Za a kara mafi karancin albashi

Abubakar Malami ya ce dukkansu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N110,000.

Malami, wanda shi ne ɗan takarar ADC a jihar Kebbi, ya ce wannan albashin zai shafi ma’aikata a dukkan jihohin Arewa maso Yamma bakwai idan suka samu nasara a zaɓen 2027.

Ya zargi gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da gaza kare al’umma da kuma aiwatar da ayyukan da za su taimaka wajen fitar da mutane daga talauci.

ADC ta bayyana dalilin taron

Malami ya ce an zaɓi ranar Laraba ne saboda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da fara kamfen ɗin zaɓen, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Ya ce ’yan takarar ADC na Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara sun amince da yarjejeniyar da ta shafi tsaro, ci gaba da kuma samun ci gaban tattalin arziki tare.

Kara karanta wannan

Dan takara ya yi alkawarin samar da lantarki a kowane gida cikin watanni 11 a Najeriya

Malami ya bayyana matsalar tsaro

Malami ya ce yankin Arewa maso Yamma yana fuskantar matsaloli masu tsanani, inda ya yi zargin cewa sama da mutane 16,000 sun rasa rayukansu sakamakon rashin tsaro tsakanin Yunin 2023 da Agustan 2026.

Ya kuma ce an samu sama da hare-haren garkuwa da mutane 1,583 tun daga watan Janairun 2023, lamarin da ya yi zargin ya kai ga sace sama da mutane 10,000 daga gidajensu da gonakinsu.

A cewarsa, dubban iyalai sun rasa matsugunansu, yayin da sama da hekta 533,000 na gonaki a Zamfara da Katsina kaɗai suka zama babu kowa a cikinsu.

Ya kuma ce yankin Arewa maso Yamma na da kashi 45 cikin 100 na yaran Najeriya da ba sa zuwa makaranta.

Ya ce rashin tsaro ya jefa mutane cikin yunwa

Malami ya ce rashin tsaro ya tilasta wa manoma barin gonakinsu, wanda hakan ya haifar da ƙarancin abinci tare da hana yara damar zuwa makaranta.

Kara karanta wannan

Babbar magana: NNPP ta gano wanda zai ci amana tsakanin Kwankwaso da Peter Obi

Ya ce rashin ilimi kuma na iya ƙara yawan mutanen da za su iya shiga ƙungiyoyin ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka nan gaba.

Saboda haka, ya ce ’yan takarar sun ɗauki alƙawarin sauya salon mulki domin gwamnati ta iya magance matsalolin yankin cikin inganci tare da dawo da zaman lafiya da tsaro.

An ce an samu N8.33tr daga asusun tarayya

Malami ya ce jihohi da ƙananan hukumomi a yankin sun samu sama da N8.33trn a matsayin rabon kuɗin tarayya tsakanin Yunin 2023 da Agustan 2026.

Sai dai ya yi zargin cewa duk da wannan kuɗi, har yanzu bai zama ingantaccen sufuri, abinci mai sauƙin samu, kiwon lafiya mai araha, makarantu masu aiki da kuma ingantaccen yanayin rayuwa ga al’umma ba.

Ya ce shi da sauran ’yan takarar sun amince da ɗaukar matakai na musamman domin sauya wannan yanayi.

Yan takarar ADC sun yi alkawari
'Yan takarar gwamnan ADC na jihohin Arewa maso Yamma tare da Atiku Abubakar Hoto: Walin Sokoto Media Team
Source: Facebook

An kai hari gidan shugaban ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun kai hari gidan shugaban jam’iyyar ADC a jihar Edo, Kennedy Odion.

Maharan sun kutsa gidan Odion da ke kusa da Winners Road, Uhie, a birnin Benin, da misalin ƙarfe 3:00 na dare ranar Lahadi, 6 ga watan Satumban 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng