Adebayo Ya Kada Hantar APC da Tinubu, Ya Fadi Yadda Za Su Zo na Karshe a 2027

Adebayo Ya Kada Hantar APC da Tinubu, Ya Fadi Yadda Za Su Zo na Karshe a 2027

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP, Adewole Adebayo, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba wanda ba za a iya kayarwa ba ne a zaɓen 2027
  • Adebayo ya ce APC za ta zo ta ƙarshe, yana mai cewa sakamakon zaɓen zai dogara ne kan ƙuri’un da ’yan Najeriya za su jefa
  • Ɗan takarar ya ce Najeriya na da damar noma da za ta iya ba Afirka abinci, amma rashin isasshen jari ya hana bunƙasar fannin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Adewole Adebayo, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ba wanda ba za a iya kayarwa ba ne a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Adebayo ya kuma yi hasashen cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki za ta zo ta ƙarshe a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa ya gano abin da ya hana a magance rashin tsaro a Najeriya

Adebayo ya hango rashin nasarar Tinubu
Adewole Adebayo na SDP da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga, Prince Adewole Adebayo
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne ranar Talata, 8 ga watan Satumban 2026 yayin wata hira da shirin Politics Today na Channels Tv inda aka tambaye shi kan damar da yake da ita ta kayar da Tinubu.

Ya ce masu zaɓe ne za su yanke hukunci

Adebayo ya ce waɗanda ke ganin Tinubu da APC ba za a iya kayar da su ba suna raina ƙarfin masu zaɓe a Najeriya.

Ya jaddada cewa sakamakon zaɓen zai kasance bisa ƙuri’un da ’yan Najeriya za su jefa, ba wai ƙarfin gwamnati ko jam’iyya ba.

“Waɗannan mutane suna cin mutuncin ’yan Najeriya. Ba za ka iya kasancewa a gwamnati ba idan ba ’yan Najeriya suka zaɓe ka,” in ji Adebayo.

Ya ce aikinsa shi ne isar da saƙonsa ga ’yan Najeriya, musamman kan buƙatar kawo ƙarshen talauci da rashin tsaro.

A cewarsa, idan mutane suka amince da wannan saƙo kuma suka zaɓe shi, APC za ta zo ta ƙarshe saboda za a ƙirga yawan ƙuri’un da kowane ɗan takara ya samu.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta fallasa shirin da aka yi wajen tarbar dumbin mutane zuwa APC a Kano

Adebayo ya yi magana kan raba kayan tallafi

Ɗan takarar ya ce masu zaɓe za su iya ƙin karɓar kayan tallafi ko kuɗi idan hankalinsu ya koma kan matsalolin da suke son a magance.

“Idan mutane ba sa karɓar shinkafa da kuɗi daga gare su, kuma kuka mayar da hankali kan abin da ya kamata a yi domin ceto wannan ƙasa daga talauci da rashin tsaro na har abada, za mu yi nasara da yardar Allah,” in ji shi.

Adebayo ya ce ’yan Najeriya ba za su iya jure ƙarin shekaru huɗu na irin wannan yanayi ba, saboda a cewarsa, matsalolin da ake fuskanta sun yi wa al’umma yawa.

Ya ce Najeriya na iya ciyar da Afirka

Da yake magana kan manufofinsa, Adebayo ya ce Najeriya na da isasshen ƙarfin noma da zai ba ta damar zama babbar mai samar da abinci ga ƙasashen Afirka. Ya ce idan aka yi wa fannin noma isasshen jari, Najeriya za ta iya ciyar da daukacin nahiyar Afirka cikin shekaru uku.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa zai mayar da litar fetur N200, ya fadi abin da ya shirya

“Mu ƙasa ce da ke da damar ciyar da Afirka baki ɗaya cikin shekaru uku. Babu isasshen jari a fannin noma,” in ji shi.
Adebayo ya hango rashin nasarar APC
Adewole Adebayo na jawabi a wajen taro Hoto: Prince Adewole Adebayo
Source: Twitter

Mariya ta ce Tinubu zai ba dan APC mulki a 2031

A wani labarin kuma, kun ji cewa karamar ministar harkokin Abuja, Mariya Mahmud ta hango nasarar jam’iyyarsu ta APC har bayan zaben 2027.

Mariya Mahmud ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa kuma APC za ta sake yin nasara a shekarar 2031.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng