Lauya Ta Fayyace Gaskiya kan Zargin Sheikh Gumi Ya Kwace Matar da Aka Auro a Morocco

Lauya Ta Fayyace Gaskiya kan Zargin Sheikh Gumi Ya Kwace Matar da Aka Auro a Morocco

  • Lauyar Khadija Diab ta ce tana Morocco tun Afrilu 2026, bayan ƙungiyarta ta taimaka mata samun takardar tafiya saboda zargin mijinta ya riƙe fasfo ɗinta
  • Khadija ta kai ƙorafi kan zargin cin zarafi a cikin aure, rashin isasshen abinci da kulawa, tare da wasu matsaloli na zamantakewar aure
  • Lauyar ta karyata zargin cewa Sheikh Ahmad Gumi na riƙe da Khadija, tana mai cewa matar tana zaune tare da iyalanta a Morocco

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Lauyar wata ‘yar kasar Morocco, Khadija Diab, ta musanta ikirarin mijin matar, Nasiru Idris Musa, cewa tana tare da malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi.

Lauyar, Bilkisu Abdulrasheed Chedi, ta bayyana cewa Khadija tana Morocco tun watan Afrilu 2026, inda take zaune tare da iyalanta.

Lauya ta fito ta kare Sheikh Gumi
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi na gabatar da karatu Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Khadija tana tare da iyalanta a Morocco

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya dauki zafi bayan an yi wa Peter Obi ruwan duwatsu a Benue

Lauyar ta bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafinta Facebook da aka tantance na Dr Ahmad Gumi a ranar Talata, 8 ga watan Satumban 2026.

Ta ce Khadija ta koma Morocco a watan Afrilu, kuma iyalanta sun tabbatar wa ƙungiyar cewa ta isa ƙasar lafiya kuma tana zaune tare da su.

Chedi, wadda ita ce shugabar ƙungiyar Women Aware of Rights Initiative, ta ce ƙungiyar ta taimaka wa Khadija samun takardar tafiya ta gaggawa bayan zargin cewa mijinta ya ƙwace fasfo ɗinta na ƙasa da ƙasa.

Chedi ta ce Khadija ta shafe kusan watanni shida a Morocco, saboda haka zargin cewa tana tare da Sheikh Gumi ba shi da tushe.

“Dukkan zarge-zargen cewa tana tare da Sheikh Gumi ƙarya ne kuma ba su da tushe, domin ba zai yiwu mutum ya kasance a ƙasashe biyu daban-daban a lokaci guda ba,” in ji lauyar.

Zargin cin zarafi a cikin aure

Chedi ta ce Khadija ta tuntubi Women Aware of Rights Initiative a watan Oktoban 2025, inda ta zargi mijinta da aikata mata munanan abubuwa a cikin aure.

Kara karanta wannan

Janar Christopher Musa ya kira ruwa, lauyoyin El Rufai sun nemi N10bn da wasu bukatu

A cewarta, Khadija ta yi zargin fuskantar cin zarafi a gida, rashin isasshen abinci da kulawa, da kuma abin da ta bayyana a matsayin “alaƙar aure da ba ta dace da doka ko ɗabi'a ba”.

Lauyar ta ce ƙungiyar ta shawarci Khadija da yin gwaje-gwajen lafiya, bayan da ta gabatar da zarge-zargen nata.

Ta ce sakamakon gwaje-gwajen ya nuna cewa Khadija ta kamu da wasu cututtukan da ake iya yaɗawa ta hanyar jima'i.

An kai ƙarar batun kotu

Chedi ta ce daga baya Khadija ta bayyana cewa ba ta son ci gaba da zaman aure, tana zargin mijinta da cin zarafinta.

Ta ce an shigar da ƙara a madadinta a Kotun Shari’a ta Daura Road da ke Kaduna, inda aka fara sauraron batun a ranar 3 ga Oktoban 2025.

A cewar lauyar, an ɗage shari’ar zuwa ranar 11 ga Nuwamba 2025 bayan lauyan wanda ake ƙara ya gabatar da buƙatar sulhu.

Daga baya, tsarin shari’ar ya samu tsaiko bayan wanda ake ƙarar ya sauya lauyansa, yayin da sabon lauyan ya kalubalanci ikon kotun na sauraron shari’ar.

An taimaka mata ta koma Morocco

Chedi ta ce rashin halartar lauyoyi a wasu zaman kotu da kuma yajin aikin ma’aikatan shari’a a Kaduna sun ƙara jinkirta shari’ar.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa ya gano abin da ya hana a magance rashin tsaro a Najeriya

Ta ce daga baya Khadija ta shiga cikin matsanancin damuwa, sannan ta bayyana sha’awarta ta komawa gida Morocco.

Saboda zargin cewa mijinta na riƙe da fasfo ɗinta na ƙasa da ƙasa, ƙungiyar ta taimaka mata wajen samun takardar tafiya daga gwamnatin Morocco.

Ta ce jami’an shige da fice na Morocco sun tabbatar da cewa Khadija ta isa ƙasar lafiya, yayin da Ofishin Jakadancin Morocco da ke Najeriya ma ya sanar da ƙungiyar cewa ta isa.

An sake shigar da ƙarar neman raba aure

Lauyar ta ce kafin Khadija ta bar Najeriya, ta ba ta izinin ci gaba da bin shari’ar a madadinta.

Chedi ta bayyana cewa an dakatar da shari’ar da ke gaban Kotun Shari’ar Daura Road a ranar 10 ga Yunin 2026.

Ta ce daga baya an sake shigar da wata sabuwar ƙara a watan Yulin 2026, inda aka nemi kotu ta raba auren Khadija da mijinta bisa dokar Musulunci. Lauyar ta bukaci jama'a da su yi watsi da ikirarin cewa Sheikh Gumi na riƙe da Khadija.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa zai mayar da litar fetur N200, ya fadi abin da ya shirya

Lauyar ta ce manufar bayanin nata ita ce warware zare da abawa da kuma bayyana gaskiyar abin da ya faru game da inda matar take.

An kare Sheikh Gumi kan zargin kwace matar aure
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi a wajen karatu Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Gumi ya sake magana kan sulhu

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannen malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya sake yin magana game da zama da ƴan ta'adda.

Malamin ya kuma yin kira da a tattauna da kungiyoyin masu dauke da makamai, yana tambayar dalilin da ya sa ba a yi wa 'yan Boko Haram da masu garkuwa irin tsarin da aka yi wa mayaƙan Neja Delta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng