'Yan Bindiga Sun Yi Barna da Suka Farmaki Gidan Shugaban Jam'iyyar ADC

'Yan Bindiga Sun Yi Barna da Suka Farmaki Gidan Shugaban Jam'iyyar ADC

  • Yan bindiga sun kutsa gidan shugaban ADC a Edo, Kennedy Odion, inda suka tafi da tsabar kudade, wayoyin hannu huɗu da wasu kayayyaki
  • Maharan sun sace motoci biyu kirar Toyota Highlander daga gidan shugaban jam’iyyar da ke yankin Uhie, Benin City, da sanyin safiyar Lahadi
  • ’Yan sanda sun ƙaddamar da farautar waɗanda ake zargi, yayin da sashen VCRU ya karɓi binciken domin gano tare da kama waɗanda suka aikata laifin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Edo - Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun kai hari gidan shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Edo, Kennedy Odion.

Maharan sun kutsa gidan Odion da ke kusa da Winners Road, Uhie, a birnin Benin, da misalin ƙarfe 3:00 na dare ranar Lahadi, 6 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun fatmaki mutane ana shirin yin sallah, an rasa rayukan bayin Allah

'Yan bindiga sun kai hari a Edo
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Lamarin ya faru ne a ranar 6 ga Satumba, 2026, inda maharan suka yi awon gaba da kuɗi da motoci da kuma wasu kayayyaki masu daraja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Abubuwan da aka sace a gidan shugaban ADC

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Edo, ASP Eno Ikoedem, ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa.

Ta ce maharan sun tafi da wayoyin hannu guda huɗu, tsabar kudi N500,000 da motoci biyu kirar Toyota Highlander.

Baya ga waɗannan, maharan sun kuma kwashe wasu kayayyaki masu daraja daga gidan shugaban jam’iyyar ADC.

Ikoedem ta ce bayan samun rahoton, rundunar ’yan sanda ta fara farautar waɗanda ake zargin da hannu wajen kai harin.

Kwamishinan ’yan sanda ya ziyarci wurin

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Edo, CP Patrick Daaor, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru.

Ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano tare da cafke mutanen da suka kai harin.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An cafke likitoci, lauyoyi da masu ba 'yan bindiga bayanai

Mai magana da yawun rundunar ta ce an miƙa binciken ga Violent Crime Response Unit (VCRU), wani sashe na rundunar da ke mayar da hankali kan manyan laifuka masu alaƙa da tashin hankali.

“An miƙa shari’ar ga Violent Crime Response Unit (VCRU), yayin da jami’an bincike suka gudanar da binciken wurin da lamarin ya faru tare da fara bincike,” in ji Ikoedem.

’Yan sanda sun fara farautar maharan

Rundunar ’yan sandan ta ce jami’an bincike sun fara tattara bayanan da za su taimaka wajen gano waɗanda suka kai harin.

Har zuwa lokacin fitar da rahoton, ba a bayyana ko an kama wani mutum da ake zargi da hannu wajen fashin ba. Rundunar ta ce za ta ci gaba da bincike domin tabbatar da kama waɗanda suka aikata laifin da kuma gurfanar da su gaban kotu.

'Yan bindiga sun kai hari a Edo
Taswirar jihar Edo, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jami'an tsaro sun hallaka hatsabibin dan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa al'ummar wasu yankuna a jihar Zamfara sun samu sauki bayan hallaka daya daga cikin hatsabiban yan bindiga wanda ya kasance mai hatsari a yankin.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa wani daga cikin manyan yan bindiga, Kachalla Auta ya mutu yayin arangama da jami'an tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng