Kwankwaso Ya Dauki Zafi bayan an Yi Wa Peter Ruwan Duwatsu a Benue
- Rabiu Kwankwaso ya yi Allah-wadai da tare ayarin Peter Obi yayin da yake kan hanyar zuwa Benue, yana bayyana lamarin a matsayin barazana ga dimokuraɗiyya
- Tsohon gwamnan na Kano ya bukaci gwamnatin Benue ta tabbatar da tsaron Obi da tawagarsa, tare da ba su damar gudanar da zirga-zirga cikin ’yanci
- Masu zanga-zanga sun tare hanyar Gboko a Makurdi, suna rera “Ba ma son Peter Obi,” lamarin da ya hana ayarinsa ci gaba da tafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na National Democratic Congress (NDC), Rabiu Kwankwaso, ya yi magana kan tare ayarin Peter Obi a jihar Benue.
Sanata Kwankwaso ya yi Allah-wadai da tare ayarin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, a lokacin da yake tafiya Benue.

Source: Facebook
Kwankwaso ya bayyana matsayarsa ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, 8 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan
Halin da ake ciki da yan sanda suka tabbatar da hari kan ayarin motocin Peter Obi
Tsohon gwamnan na Kano ya bayyana lamarin a matsayin abin da ke barazana ga dimokuraɗiyya, inda ya bukaci gwamnatin Benue ta gano tare da gurfanar da waɗanda suka shirya tare ayarin.
“Rana ce mara kyau ga dimokuraɗiyya”
Kwankwaso ya ce zargin tara mutane domin tare ayarin Obi da hana shi shiga Makurdi “rana ce mara kyau ga dimokuraɗiyyarmu.”
Ya jaddada cewa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bai wa kowane ɗan ƙasa ’yancin zirga-zirga a cikin ƙasar.
“Hukumomi su tuna cewa Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar wa kowane ɗan ƙasa ’yancin zirga-zirga. Wannan haƙƙi ya fi dacewa da Mista Obi, kasancewar tsohon gwamna ne kuma fitaccen ɗan adawa,” in ji Kwankwaso.
Kwankwaso ya bukaci a kare Obi
Kwankwaso ya bukaci gwamnatin Jihar Benue da ta tabbatar da tsaron Peter Obi da kuma sauran mutanen da ke cikin tawagarsa.
Ya kuma yi kira ga Shugaban Ƙasa da ya gargadi gwamnonin jihohi, musamman waɗanda ke cikin jam’iyyarsa, kan duk wani mataki da zai iya raunana dimokuraɗiyya.
“Ina kuma kira ga Shugaban Ƙasa da ya gargadi gwamnonin jihohi, musamman waɗanda ke cikin jam’iyyarsa, kan duk wani mataki da zai iya raunana martabar dimokuraɗiyyarmu,” in ji shi.
Ya nemi ƙasashen duniya su lura
Tsohon gwamnan Kano ya kuma yi kira ga ƙasashen duniya, ciki har da ofisoshin jakadanci da ƙungiyoyin sa ido kan zaɓe, da su lura da abin da ya faru.
Ya bukace su da su ƙarfafa hukumomin Najeriya wajen tabbatar da bin doka, kare ’yan siyasar adawa da kuma tabbatar da ’yancin dimokuraɗiyya.
Masu zanga-zanga sun tare hanyar Gboko
Tun da farko Legit Hausa ta ruwaito cewa an hana Peter Obi ci gaba da tafiya a Benue bayan wasu masu zanga-zanga sun tare hanyar Gboko a Makurdi, babban birnin jihar.
Masu zanga-zangar sun rera taken “Ba ma son Peter Obi”, yayin da suka tare hanyar da ke kusa da sansanin Sojojin Sama na Najeriya da filin jirgin saman Makurdi.
An shafe sa’o’i ana tare hanyar, lamarin da ya kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa tare da hana ayarin Obi ci gaba da tafiya.

Kara karanta wannan
Dan takarar shugaban kasa ya gano abin da ya hana a magance rashin tsaro a Najeriya

Source: Original
NNPP ta gargadi Obi kan Kwankwaso
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar NNPP ta gargadi NDC da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, kan Sanata Rabiu Kwankwaso.
Jam’iyyar ta ce bambance-bambancen siyasar da suka samu tsakaninta da Kwankwaso bayan zaɓen 2023 ya kamata ya zama babban darasi ga NDC.
Asali: Legit.ng
