U 17: Najeriya ta kafa tarihi da ta lashe gasar cin kwallon kafa a duniya
- Najeriya ta doke Japan da ci 2-1, ta lashe gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekara 17
- Tawagar Flamingos ta kafa tarihi, inda ta zama kasa ta farko a nahiyar Afrika da ta lashe wannan kofi
- A tarihi wannan ne karon farko da kasar Najeriya ta lashe gasar tun bayan fara fafatawa a cikinta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Morocco - Najeriya ta doke Japan da ci 2-1, hakan yana nufin ta lashe gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekara 17.
Tawagar matan Najeriya, wadda aka fi sani da Flamingos, ta kafa tarihi bayan ta doke Japan da ci 2-1 a wasan karshe na gasar 2026.
Kwallon kafa: Najeriya ta lashe gasar U-17
Rahoton The Cable ya ce Najeriya ta yi nasara a gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekara 17 da aka gudanar a kasar Morocco.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta yi bayani kan shafukan da mutum zai shiga domin samun tallafin N50,000
A yau ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026 aka yi wasan karshe, wanda ya kawo karshen wannan gasa.
'Yar wasan Najeriya, Awawu Bashiru mai wasa a tsakiyar fili ce ta fara zura kwallo a ragar Japan a minti na 38 na farkon wasan.
Awawu Bashiru ta doki kwallon daga nesa a karshe kuma wanda ta ke tsaron ragar Japan ta kasa rike kwallon har ta shiga cikin zare.
Awawu da Umejiaku sun leka ragar Japan
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, Oluebube Umejiaku ta kara zura kwallo ta biyu a ragar Japan, ta samu ta wuce mai tsaron raga.
Japan ta samu kwallon rage tazarar ci ta hannun Ito a minti na 85 a zagaye na biyu, amma hakan bai hana Najeriya samun nasara ba.
Duk da yadda 'yan kwallon kasar Japan suka huro wuta, ba su iya kara jefa kwallo a ragar Najeriya ba.
Wannan nasara ta sa Najeriya ta zama kasa ta farko a nahiyar Afirka da ta lashe kofin duniya na mata 'yan kasa da shekara 17 da haihuwa.

Kara karanta wannan
“Ko zai shafi Tinubu a 2027?” Yadda al’ummar Legas suka tarbi Kwankwaso ya ja hankali
'Yan kwallon Najeriya sun bar tarihi a gasar U-17
Leadership ta ce haka kuma, wannan shi ne karon farko da tawagar Flamingos ta lashe wannan gasa, bayan da ta kai zagayen karshe a tarihi.
A wasan kusa da na karshe, Najeriya ta lallasa Brazil da ci 3-1, yayin da Japan ta samu tikitin zuwa wasan karshe bayan ta doke Koriya ta Arewa.
Asali: Legit.ng