Zaben 2027: Wike Zai Raba Biliyoyi don Tabbatar da Tazarcen Tinubu
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi alƙawarin ba duk kansilan da ya tabbatar da nasarar APC a mazabarsa Naira miliyan 10
- Wike ya bukaci kansiloli su haɗa kai da shugabannin al'umma, ƙungiyoyin matasa da sauran masu ruwa da tsaki domin tallafa wa APC a zaɓen 2027
- Ministan ya zargi ’yan adawa da munafunci kan yadda suke kallon hukuncin kotu, yana mai cewa suna yaba wa shari'a idan ta yi musu daidai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi alƙawarin ba duk kansilan da ya tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a mazabarsa Naira miliyan 10 a babban zaɓen 2027.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamban 2026 yayin wani taron masu ruwa da tsaki na Rainbow Coalition da aka gudanar a ƙaramar hukumar Kwali, Abuja.

Source: Facebook
Wike ya yi alƙawarin N10m ga kansiloli
Rahoton tashar Channels tv ya ce taron ya samu halartar sarakunan gargajiya, masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da kuma mazauna yankin.
Ministan ya buƙaci kansilolin da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan al'umma da kuma haɗa ƙungiyoyin jama'a domin tabbatar da nasarar APC a mazabunsu.
“Duk kansilan da ya kai wa jam’iyya nasarar mazabarsa zai samu ladan Naira miliyan 10. Saboda haka, ku je ku gana da shugabanninku, ƙungiyoyin matasa da sauran ƙungiyoyi. Mu tabbatar mun kai wa Mai Girma Shugaban Ƙasa nasarar mazabarmu.” In ji shi.
Ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu
Ministan ya kuma bayyana goyon bayansa ga ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na neman wa'adi na biyu a zaɓen 2027.
Haka kuma, ya amince da takarar Sanata Philip Aduda domin kujerar Sanatan Abuja, da kuma Danladi Chiya domin kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazabar Abuja ta Kudu.
Wike ya ce ba ya buƙatar ƙara yin dogon jawabi domin gamsar da al'ummar yankin, yana mai cewa ya kamata su yi la'akari da ayyukan da ake gani maimakon alkawuran da ba a cika ba.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa ƙananan hukumomin Kwali, Gwagwalada da Abaji za su marawa APC baya a zaɓen da ke tafe.
Wike ya zargi ’yan adawa da munafunci
A wani ɓangare na jawabinsa, Wike ya zargi wasu ’yan siyasa da jam’iyyun adawa da nuna bambancin ra'ayi kan hukuncin kotuna, gwargwadon ko hukuncin ya yi musu daidai ko akasin haka, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Ya soki yadda wasu ’yan adawa ke sukar hukuncin kotu, inda ya yi tsokaci kan hukuncin da ya soke tikitin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar.
Wike ya kwatanta yadda ’yan adawa suka mayar da martani kan hukuncin kotu daban-daban, yana mai cewa suna yabon ɓangaren shari'a idan hukuncinsa ya amfane su.
Ya ce a lokacin da ADC ta samu nasara a wata shari'a a Kotun Ƙoli, wasu sun bayyana kotu a matsayin mafakar dimokuraɗiyya tare da yaba wa tsarin shari'ar ƙasar.
Sai dai a cewarsa, da zarar hukuncin kotu ya saba wa muradunsu, sai su fara zargin Shugaban Ƙasa da amfani da kotuna wajen yaƙar ’yan adawa.
Wike ya tambayi dalilin da ya sa wasu ’yan siyasa ke kallon kotuna a matsayin masu adalci idan hukuncinsu ya amfane su, amma su zarge su da lalata dimokuraɗiyya idan sun sha kaye a shari'a.

Source: Facebook
Wike ya caccaki Amaechi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Nyesom Wike, ya ce bai kamata a zaɓi tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin mataimakin shugaban kasa ba. Wike ya ce ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na ADC.
Rt. Hon. Chibuike Amaechi, bai cancanci rike kowane muƙami a ƙasar ba saboda zargin rashin kyakkyawan kula da kuɗaɗen gwamnati.
Asali: Legit.ng


