Masarautar Kano Ta Yi Rashi, Babban Mai Rike da Sarauta Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Alhaji Shehu Kabiru Bayero, hakimin Dorayi kuma mai rike da sarautar Barden Kerarriyar Kano, ya rasu a ƙasar Masar
- Marigayin ya taɓa yin hakimi a Takai da Gwarzo bayan marigayi Sarki Ado Bayero ya naɗa shi Barde Kerarriyar Kano a shekarar 2006
- Bayero ya yi aiki da ’yan sandan Najeriya tsawon shekaru 35, inda ya kai matsayin kwamishinan ’yan sanda kafin ya yi ritaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Alhaji Shehu Kabiru Bayero, shugaban gundumar Dorayi da ke Kano, kuma mai riƙe da sarautar gargajiya ta Barden Kerarriyar Kano.
Alhaji Shehu Kabiru Bayero ya yi bankwana da duniya ne a ƙasar Masar kamar yadda aka sanar a ranar Talata, 8 ga watan Satumban 2026.

Source: Original
Masarautar Kano ce ta sanar da rasuwar marigayin a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata, 8 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan
'Neman fitina yake yi': Gwamnatin Benue ta yi martani mai zafi bayan jifan Peter Obi
Masarautar ta yi addu'ar Allah Ya ji ƙan marigayin, Ya ba shi hutu na har abada, sannan Ya bai wa iyalansa da gidan sarautar Kano haƙurin jure wannan babban rashi.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana lokacin da za a dawo da gawar marigayin Najeriya domin gudanar da jana’izarsa ba.
An naɗa shi hakimin Dorayi
An sauya wurin aikin Bayero daga Gwarzo zuwa sabuwar gundumar Dorayi a shekarar 2025, bayan da Sarki Muhammadu Sanusi II ya dawo kan karagar mulkin Kano.
A shekarar 2006, marigayi Sarki Ado Bayero ne ya fara naɗa shi sarautar Barde Kerarriya, sannan aka tura shi Gundumar Takai da ke ƙaramar hukumar Takai.
Daga baya, an sake sauya shi zuwa Gwarzo, inda ya ci gaba da gudanar da ayyukan sarautarsa kafin daga bisani aka tura shi Dorayi.
Ya yi shekaru 35 a rundunar ’yan sanda
Kafin shiga harkokin sarautar gargajiya, Shehu Kabiru Bayero ya yi dogon aiki a rundunar ’yan sandan Najeriya.

Kara karanta wannan
Janar Christopher Musa ya kira ruwa, lauyoyin El Rufai sun nemi N10bn da wasu bukatu
Ya shiga rundunar a shekarar 1970 a matsayin ɗan sanda mai ƙaramin matsayi, wato Police Constable.
A tsawon shekaru 35 da ya yi yana aiki, ya samu ƙarin girma har ya kai matsayin Kwamishinan ’Yan Sanda.
Ya kuma yi aiki a matsayin kwamishinan ’yan sanda a jihohin Gombe da Osun, kafin ya yi ritaya daga aikin.
Tarihin mahaifinsa
Mahaifin marigayin, Kabiru Bayero, shi ma ya riƙe babban matsayi a harkar tsaro. Daga baya, Sarki Muhammadu Sanusi I ya naɗa shi Barde Kerarriya.
A shekarun 1950, ɗan’uwansa, marigayi Sarki Ado Bayero, ya gaje shi a matsayin shugaban ’yan sandan yanki.
Rasuwar Shehu Kabiru Bayero ta kasance babban rashi ga iyalansa, Masarautar Kano da al’ummar da ya jagoranta a tsawon shekarun da ya yi yana hidima.

Source: Facebook
Sanata Bello Mandiya ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Sanatan da ya wakilci Katsina ta Kudu, Sanata Bello Mandiya, ya rasu a babban birnin tarayya Abuja.
Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda ya bayyana rasuwar Mandiya a matsayin babban rashi musamman ga al'ummar Katsina ta Kudu da kuma 'yan siyasar jihar.
Asali: Legit.ng