Abin da Ya Fi ba Abba Kabir Haushi kan Rigimarsa da Matarsa, Zainab Kwankwaso

Abin da Ya Fi ba Abba Kabir Haushi kan Rigimarsa da Matarsa, Zainab Kwankwaso

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana yadda dangantakarsa da matarsa Zainab Musa Kwankwaso ta shiga matsala
  • Abba ya ce an fitar da kayan matarsa daga gidansa sannan aka ɗauke ta ba tare da an sanar da shi ba
  • Gwamnan ya bayyana cewa sun shafe kusan shekaru 20 da aure, sun haifi yara shida, kuma har yanzu akwai fatan samun sulhu a tsakaninsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi karin haske kan rikicin da ya shiga tsakaninsa da matarsa, Zainab Musa Kwankwaso.

Gwamnan ya bayyana wasu abubuwan da suka faru a zamantakewarsu kafin matsalar ta kai ga shigar da ƙara a kotu.

Abba Kabir ya magantu kan rigimarsa da matarsa
Zainab Kwankwaso da Gwaman Abba Kabir. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa, inda ya yi ƙoƙarin fayyace dalilan da suka jawo rashin jituwar tsakaninsa da matar tasa.

Kara karanta wannan

'Asirina zai tuno': Gwamna ya ce zai shiga matsala idan Tinubu ya faɗi zaɓe

Bayanin nasa ya biyo bayan kalaman da ya yi a wani taron 'yan fansho da aka gudanar a Kano ranar Litinin, 16 ga Nuwambar 2026, waɗanda suka tayar da muhawara a sassan Arewacin Najeriya.

A baya dai rahotanni sun bayyana cewa Zainab ta garzaya wata kotu a Abuja domin neman a raba aurenta da gwamnan, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce saboda alaƙar iyali da siyasa da ke tsakaninta da Rabiu Musa Kwankwaso.

Yadda matsalar aurensu ta samo asali

A yayin tattaunawar, Abba Kabir ya bayyana cewa matsalolin da suka dabaibaye aurensu ba ƙaramin abu ba ne, yana mai cewa ya daɗe yana fuskantar wasu abubuwa ba tare da ya fito ya yi magana a kansu ba.

Ya bayyana cewa Zainab 'yar gidan Rabiu Musa Kwankwaso ce, wanda ya fara aurar da ita kafin daga baya ita da gwamnan suka yi aure kimanin shekaru 20 da suka wuce.

A cewarsa, sun yi zaman aure na tsawon lokaci tare da samun 'ya'ya, amma daga baya abubuwa suka sauya, har aka kai ga fitar da kayanta daga gidansa.

Gwamnan ya ce duk da abin da ya faru, bai ɗauki matakin fitowa fili ya yi bayanin lamarin ba, domin ya zaɓi yin shiru da haƙuri.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya fadi matakin da ya kamata El Rufa'i ya dauka kafin tsare shi

Ya bayyana cewa ya ma sanar da yaransu cewa mahaifiyarsu za ta sake dawowa gidansu, amma daga baya sai ya samu labarin cewa ta shigar da ƙara a kansa a wata kotu da ke Abuja.

Abba ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda lamarin ya faru, yana mai cewa yana da cikakkun bayanai da shaidu game da yadda aka fitar da matar tasa daga gidansa.

Sai dai ya ce ba ya son bayyana wa jama'a dukkan bayanan da suka shafi yadda aka gudanar da lamarin.

Dalilin da ya sa ya fito ya yi magana

Da aka nemi jin dalilin da ya sa ya yi maganar rikicin aurensa a bainar jama'a, gwamnan ya ce bai kamata a ɗora masa laifin siyasantar da matsalar ba.

Ya bayyana cewa duk wanda aka yi wa irin abin da ya faru da shi zai ji rauni, musamman idan aka yi wa iyalinsa wasu abubuwa ba tare da saninsa ko yardarsa ba.

A bayaninsa, ya ce an kwashe kayan iyalinsa daga gidansa, aka ɗauke matarsa zuwa wani gida ba tare da saninsa ba, sannan daga baya ya samu labarin cewa ita ce ta shigar da ƙara a kansa.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Ganduje ya nuna inda sabanin Abba da matarsa ya samo asali

Gwamnan ya jaddada cewa yana da bayanai kan yadda waɗannan abubuwa suka gudana, amma ba zai bayyana komai ga jama'a ba.

Duk da haka, ya bayyana cewa ana duba yiwuwar warware matsalar, yana mai fatan cewa za a iya cimma matsaya ta hanyar sulhu.

Karin bayani na tafe ....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.