Siyasa ba da Gaba ba; Tawagar PDP Ta Ziyarci Kusoshin APC da Suka Yi Hatsari a Gombe

Siyasa ba da Gaba ba; Tawagar PDP Ta Ziyarci Kusoshin APC da Suka Yi Hatsari a Gombe

  • Tawagar PDP ƙarƙashin jagorancin Dan’azumi Adamu Pindiga ta ziyarci shugabannin APC da suka jikkata a hatsarin mota a Gombe
  • Daga cikin waɗanda suka jikkata akwai shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na jihar, Sa’adu Hassan, da shugaban jam’iyyar, Dantata Ndus
  • PDP ta ce bambancin jam’iyya bai kamata ya hana ’yan siyasa nuna tausayi, zumunci da mutunta juna ba, musamman a lokacin da wani ya shiga matsala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - A wani mataki da ke nuna juriya a siyasa da haɗin kai, reshen jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na jihar Gombe ya kai ziyarar jaje ga shugabannin All Progressives Congress (APC) da suka jikkata a hatsarin mota.

Hatsarin ya rutsa da shugabannin APC ne a ranar Talata, yayin da suke dawowa daga gangamin yaƙin neman zaɓe.

Kara karanta wannan

Fadan manya: Bayan karyata shi, Sule Lamido ya sake taso Kashim Shettima a gaba

PDP ta tura tawaga a Gombe
Shugaban kwamitin kamfen na PDP yayin ziyarar jaje da suka je wurin 'yan APC a Gombe Hoto: Abubakar Haruna Audi
Source: Facebook

Tawagar PDP ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar, Hon. Dan’azumi Adamu Pindiga, ta ziyarci waɗanda suka jikkata a Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH), Gombe, cewar rahoton jaridar Vanguard.

An gudanar da ziyarar ne a ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, 2026, domin jajanta musu da yi musu fatan samun lafiya cikin gaggawa.

Manyan shugabannin APC da suka jikkata

Daga cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su akwai Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na jihar Gombe, Hon. Sa’adu Hassan, da shugaban APC na jihar, Hon. Dantata Ndus. Hatsarin ya kuma rutsa da wasu mambobin jam’iyyar.

Sauran waɗanda suka halarci ziyarar daga PDP sun haɗa da sakataren jam’iyyar na jiha, Hon. Adamu Abubakar; Hon. Abubakar Walama; Hon. Sani Hassan Dogarai; Hon. Hassan Santana; Hon. Abubakar Bello (Cikasoron Gombe); da Hon. Jalo Ahmed Ganga.

Saƙon jaje daga shugabannin PDP

A yayin ziyarar, Pindiga ya isar da saƙon ta’aziyya da fatan alheri a madadin shugaban PDP a jihar Gombe, tsohon gwamna Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, OON, PhD, Talban Gombe.

Kara karanta wannan

Shinkafa da wake: An kafa kwamitin kamfen Tinubu da APC cike da yan adawa

Ya kuma wakilci ɗan takarar gwamnan jam’iyyar, Farfesa Isa Ali Pantami, da daukacin mambobin PDP a jihar.

Tawagar ta yi addu’a ga Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba shugabannin jam’iyyar da sauran waɗanda hatsarin ya rutsa da su cikakkiyar lafiya, ƙarfi da samun sauƙi cikin gaggawa.

Bambancin siyasa bai kamata ya hana zumunci ba

Wakilan PDP sun jaddada cewa bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya zama sanadin lalata zumunci, mutuntaka da girmama juna tsakanin al’ummar jihar Gombe ba.

Sun bayyana cewa, duk da bambancin jam’iyyun siyasa da muradun zaɓe, ’yan siyasa har yanzu al’umma ɗaya ne, masu nauyin da ya rataya a kansu na tabbatar da zaman lafiya.

A cewarsu, duk wani mummunan lamari da ya shafi mambobin wata jam’iyya ya kamata ya jawo tausayin kowa, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.

Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ƙamari gabanin babban zaɓen 2027, kuma ta nuna muhimmancin juriya, balagar siyasa da mutunta juna tsakanin jam’iyyu da magoya bayansu.

PDP ta je jaje wajen APC a Gombe
Taswirar jihar Gombe, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Pantami ya taya 'yan APC jaje

Kara karanta wannan

Zaben 2027: ADC ta bayyana matsayarta kan takarar Atiku duk da hukuncin kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Pantamiyya Movement ta yi ta’aziyya ga iyalan wadanda hatsarin mota ya shafa a hanyar Deba zuwa Talasse a jihar Gombe, inda ta yi addu’ar Allah ya ba wadanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa.

Kungiyar Pantamiyya, karkashin jagorancin dan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalai, abokai da makusantan duk wadanda hatsarin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng