Shugaban Kasar Da Ya Fi Daukar Albashi a Duniya Zai Samu Karin Kaso 60
- Firaministan Singapore, Lawrence Wong, zai ga albashinsa na shekara ya tashi daga S$2.2m zuwa S$3.6m, wanda zai ƙara sama da kashi 60%
- Wong ya ce zai bayar da dukkan ƙarin albashin da zai samu a cikin shekaru biyar masu zuwa ga ƙungiyoyin agaji
- Gwamnati ta ce ƙarin albashin ya zama dole domin jawo ƙwararrun mutane siyasa, amma matakin ya jawo suka saboda tsadar rayuwa da rashin tabbas kan ayyukan yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Singapore - Gwamnatin Singapore ta sanar da shirin ƙara albashin ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati, ciki har da Firaminista Lawrence Wong.
Wong na daga cikin shugabannin kasar da ke karɓar mafi yawan albashi a duniya, kuma sabon ƙarin zai ƙara masa albashin shekara zuwa S$3.6m.

Source: Getty Images
A halin yanzu, Firaministan na karɓar kusan S$2.2m a shekara, amma sabon tsarin zai ƙara masa sama da kashi 60, cewar rahoton tashar BBC.
Wong ya ce zai bayar da ƙarin albashin da zai samu ga ƙungiyoyin agaji a cikin shekaru biyar masu zuwa.
Gwamnati ta kare ƙarin albashin
Firaminista Wong ya ce ƙara albashin ministoci ya zama dole domin jawo ƙwararrun mutane zuwa harkokin siyasa.
Gwamnatin Singapore ta daɗe tana kare tsarin albashi mai tsoka ga ministoci, tana mai cewa hakan na taimakawa wajen jawo ƙwararrun mutane tare da rage haɗarin cin hanci da rashawa.
Sai dai matakin ya jawo suka a ƙasar, musamman a daidai lokacin da jama’a ke fuskantar damuwa kan tsaron ayyukan yi da kuma hauhawar tsadar rayuwa.
Wong ya fi sauran shugabannin duniya albashi
Ko kafin sabon ƙarin albashin ya fara aiki, Wong ya riga ya kasance cikin shugabannin kasashe a duniya da ke karɓar mafi yawan albashi.
Bayan Wong, Shugaban Hong Kong, John Lee, na karɓar kusan $719,000 a shekara, yayin da Shugaban Switzerland, Guy Parmelin, ke karɓar kusan $606,000.
Shugaban Amurka Donald Trump na karɓar $400,000 a shekara, yayin da Firaministan Birtaniya Andy Burnham ke karɓar kusan $230,000.
Albashin ministoci ma zai ƙaru
A halin yanzu, tsarin albashin ministocin Singapore ya kai kusan S$1.1m a shekara. Sabon tsarin zai ƙara adadin zuwa kusan S$1.2m, amma Wong ya ce ana sa ran mafi yawan ministocin za su kai kusan S$1.35m kafin wa’adin gwamnatin yanzu ya ƙare.
Ya ce hakan zai danganta da irin yadda ministocin suka gudanar da ayyukansu, domin wani ɓangare na albashinsu yana dogara ne kan sakamakon ayyukan gwamnati.
Aiki da tattalin arziki na daga cikin ma’auni
Wani ɓangare na albashin ministocin yana dogara ne kan ko ƙasar ta cimma wasu manufofi da aka tsara.
Waɗannan sun haɗa da rage yawan marasa aikin yi, bunƙasa kuɗin shiga da kuma samun ci gaban tattalin arziki.
Wong ya amince cewa batun albashin ministoci ya daɗe yana jawo ce-ce-ku-ce, musamman saboda ya yi nisa da abin da mafi yawan ’yan ƙasar ke samu.
Matsakaicin kuɗin shiga na wata-wata a Singapore ya kai kusan S$5,775. Sai dai Wong ya ce gwamnati na fuskantar ƙalubale wajen shawo kan ’yan kasuwa da manyan ma’aikatan gwamnati masu ƙwarewa su bar ayyukansu su shiga siyasa.

Kara karanta wannan
"Na samu labari mara dadi"; Atiku ya haska matsalar da matasa ke fuskanta a gwamnatin Tinubu

Source: Getty Images
Albashin manyan sojoji ya karu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da sabon tsarin albashi ga jami’an Rundunar Sojin Najeriya.
Karin ya sanya manyan hafsoshin soja sun samu mafi girman adadin albashin da ake amfani da shi wajen lissafin fansho.
Asali: Legit.ng

