Da Gaske Akpabio Ya Yi 'Yan Arewa Barazanar Shan Azaba idan Tinubu Ya Fadi a 2027?

Da Gaske Akpabio Ya Yi 'Yan Arewa Barazanar Shan Azaba idan Tinubu Ya Fadi a 2027?

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi magana kan kalaman da aka jingina masa cewa za a wahalar da ’yan Arewa idan Tinubu ya fadi a 2027
  • A bayanan da aka yada, an zargi Akpabio da cewa 'yan Arewa za su ji a jikinsu idan mai girma Bola Tinubu ya sha kasa a zaben
  • Ya ce yaƙin neman zaɓen 2027 ya kamata ya ta’allaka kan manufofi, nasarori da gazawa, ba kan kalaman ƙarya da za su rura wutar rikicin kabilanci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya musanta wani bayani da aka danganta da shi cewa za a sa ’yan Arewa su sha wahala tsakanin watan Janairu da Mayu idan Shugaba Bola Tinubu ya sha kaye a zaɓen 2027.

Akpabio ya bayyana kalaman da aka jingina masa a matsayin “ƙage tsantsa”, inda ya ƙalubalanci masu yaɗa zargin da su fitar da hujjar inda da lokacin da ya furta kalaman.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ware gwamna a Arewa ya kwararo masa yabo

Akpabio ya musanta yin barazana ga 'yan Arewa
Sanata Godswill Akpabio na gabatar da jawabi Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Akpabio ya nemi a fitar da hujja

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai, Hon. Eseme Eyiboh, ya fitar ranar Laraba, 9 ga watan Satumban 2026, cewar rahoton jaridar Vanguard.

A cikin sanarwar, Akpabio ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa ya taɓa yin wannan magana.

Sanarwar ta ce babu bidiyo, sauti, jawabi, hira, sanarwar manema labarai ko rahoton kafar yaɗa labarai mai inganci da ke ɗauke da kalaman.

Ya ƙalubalanci wanda ya yaɗa zargin

Shugaban Majalisar Dattawan ya ƙalubalanci Engr. Ibrahim Umar Ammar, wanda ya ce an bayyana shi a shafinsa na Facebook a matsayin wanda ke da alaƙa da Atiku Abubakar Campaign Organisation da kuma Coordinator na ADC-NYAF a Jihar Kano.

Akpabio ya bukaci a fitar da ainihin bidiyon ko faifan sautin da ba a gyara ba wanda zai nuna inda, lokacin da kuma gaban wa ya furta kalaman.

Kara karanta wannan

Shugaban da ya nemi mata su kashe aurensu kan zaben APC ya magantu

Ya kuma bukaci a bayyana ranar da wurin da aka yi taron, tare da fitar da cikakken faifan ba wani ɓangare da aka zaɓa kawai ba.

Shugaban majalisar dattawan ya ce waɗanda suka sake yaɗa sakon kawai su bayyana tushen farko da suka samo shi daga gare shi.

Ya yi gargadi kan rura rikicin kabilanci

Akpabio ya ce adawa da gwamnati ko jam’iyya abu ne da doka ta amince da shi a tsarin dimokuraɗiyya.

Sai dai ya yi gargadin cewa bai kamata a yi amfani da kalaman ƙarya wajen rura wutar ƙiyayya da rashin jituwa tsakanin ’yan Arewa da ’yan Kudu gabanin zaɓen 2027 ba.

Ya ce ya kamata fafatawar siyasa ta 2027 ta kasance kan tarihin ayyuka, manufofi, nasarori, gazawa da kuma dabarun da ’yan takara ke da su ga makomar Najeriya.

Akpabio ya musanta yi wa 'yan Arewa barazana
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Akpabio ya kira ga 'yan Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi kira ga ‘yan Najeriya, musamman matasan Arewa.

Sanata Godswill Akpabio ya bukaci da su goyi bayan sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng