Hadimin Atiku Ya Magantu kan Rarara, Ya Fadi Yadda Tinubu Ya Zama Masa Ala Ka Kai

Hadimin Atiku Ya Magantu kan Rarara, Ya Fadi Yadda Tinubu Ya Zama Masa Ala Ka Kai

  • Tawagar Atiku Abubakar ta yi martani bayan wasu fusatattun mutane sun far wa mawakin yabon Tinubu, Dauda Kahutu Rarara, a Abuja
  • Mai magana da yawun Atiku ya ce goyon bayan da Rarara ke bai wa shugaban ƙasa haƙƙinsa ne na dimokuraɗiyya, bai kamata ya zama sanadin cin zarafinsa ba
  • Paul Ibe ya bayyana cewa siyasa ta fara nuna Tinubu na zama nauyi ga Rarara, duk da cewa ya yi Allah-wadai da harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

ABUJA — Tawagar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ta yi martani kan harin da aka kai mawaki Dauda Kahutu Rarara.

Majiyoyi sun ce an kai wa fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

Wasu matasa sun kai wa Rarara hari a Abuja
Shugaba Bola Tinubu da mawaki Dauda Kahutu@omonlakiki.
Source: Twitter

Daya daga cikin hadimin dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar a ADC, Paul Ibe ya yi martani kan lamarin a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027

Yadda aka farmaki Rarara a Abuja

An kai wa Rarara harin ne ranar Juma'a, jim kaɗan bayan kammala sallar Juma'a, inda wasu fusatattun mutane suka kewaye shi tare da yayyage masa tufafi da dukansa.

Wani faifan bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta ya nuna yadda mutanen suka far masa ta ɓangarori daban-daban, duk da kasancewar jami'an tsaro a kusa da shi.

A lokacin lamarin, Rarara na sanye da hula mai tambarin Shugaba Bola Tinubu, daga bisani ya cire ta yayin da ake ci gaba da dukansa. Daga ƙarshe, jami'an 'yan sanda da wasu masu ibada ne suka kuɓutar da shi.

Rarara: Hadimin Atiku ya yi martani kan harin

Mai ba Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai cewa goyon bayan siyasa da Rarara ke bai wa Tinubu haƙƙinsa ne na dimokuraɗiyya.

Sai dai Ibe ya yi amfani da damar wajen yin tsokaci kan siyasar Tinubu, inda ya ce shugaban ƙasar ya fara zama abin nauyi ga mawakin.

Kara karanta wannan

Matasa sun far wa wawakin siyasa, Dauda Rarara da duka a masallacin Juma'a

A cikin sanarwar da ya fitar, Ibe ya ce:

"Rarara, goyon bayan da kake bai wa Tinubu haƙƙinka ne na dimokuraɗiyya. Bai kamata hakan ya sa a mayar da kai abin kai wa hari ba. Amma a fagen siyasa, abubuwa na ƙara nuna cewa Tinubu ya zama nauyi a gare ka."

Paul Ibe ya soki tsaro a Masallacin Ƙasa

Mai magana da yawun Atiku ya kuma nuna damuwa kan yadda harin ya faru duk da tsauraran matakan tsaro da aka ɗauka a wajen sallar Juma'a.

Ya ce an girke jami'an tsaro da dama, har ma aka toshe wasu hanyoyin da ke kusa da masallacin, amma hakan bai hana wasu mutane kai wa Rarara hari ba.

Ibe ya jaddada cewa tashin hankali kan kowane mutum, ciki har da abokan hamayyar siyasa, abin Allah-wadai ne, kuma bai kamata a lamunce shi ba.

Ya ƙara da cewa bambancin ra'ayin siyasa ba hujja ba ne ta cin zarafi ko kai wa wani hari.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa

Dalung ya ja hankalin Rarara

An ji cewa tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya yi Allah-wadai da rahoton dukan mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, a masallacin Abuja.

Dalung ya ce babu wanda ya cancanci a kai masa hari saboda ra’ayinsa na siyasa ko goyon bayan gwamnatin da yake so.

Ya bukaci Rarara ya yi tunani kan halin da talakawan Najeriya ke ciki, musamman matsin tattalin arziki da suka danganta da manufofin gwamnatin da yake yabawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.