Ana tsaka da Yakin Iran, Kasar Saudiyya Ta Kai Munanan Hare Hare kan Manyan Birane 3

Ana tsaka da Yakin Iran, Kasar Saudiyya Ta Kai Munanan Hare Hare kan Manyan Birane 3

  • Kungiyar Houthi ta tabbatar da cewa jiragen yakin Saudiya sun kai hare-haren sama a lardunan Marib, al-Jawf da Taiz na kasar Yemen
  • Rahotanni sun ce hare-haren sun biyo bayan wani samame da yan Houthi suka kai kan wuraren makamashin Saudi Aramco
  • Rikicin ya zama mafi girma tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani a 2022

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Yemen - Rahotanni daga gidan talabijin na Al Masirah mai alaka da kungiyar Houthi ya ruwaito cewa jiragen yakin Saudiya na kai hare-haren sama a wasu larduna daban-daban na kasar Yemen.

Rahoton ya ce hare-haren sun shafi lardunan Marib, al-Jawf da Taiz, inda aka ruwaito cewa Saudiyya ta yi luguden wuta a yankin Khab wa Sha'af da ke lardin al-Jawf.

Jiragen Saudiyya.
Jiragen yakin rundunar sojin sama ta kasar Saudiyya Hoto: Stocktrek
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta ce sauran hare-hare guda 10 sun shafi wurare daban-daban a gundumar Sirwah da ke birnin Marib, yayin da hare-hare guda biyar suka afka yankin al-Barh da ke lardin Taiz.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya sa Majalisar kolin harkokin Musulunci ta dauki zafi a shari’ar El Rufai

Saudiyya ta kai hari a Saada

A lardin Saada kuma, an ruwaito cewa sojojin Saudiya sun kai harin bama-bamai a Ghor al-Mishwat da ke gundumar Ghamr, kusa da iyakar kasar.

Har zuwa lokacin fitar da rahoton, kawancen kasashen da Saudiya ke jagoranta a Yemen bai tabbatar da kai wadannan hare-haren ba.

Harin ya biyo bayan sanarwar da kungiyar Houthi ta yi ranar Talata cewa ta kai hari kan wasu wuraren makamashi mallakin babban kamfanin mai na Saudi Aramco a kudancin Saudiya.

Mai magana da yawun rundunar sojin Houthi ya bayyana harin a matsayin "babban farmaki".

Yadda yan Houthi suka fara kai hari

Mahukuntan Saudiya sun tabbatar da cewa an kai hare-hare kan wasu wurare da cibiyoyin da ke da alaka da bangaren makamashi a kudancin kasar.

Riyadh ta yi alkawarin mayar da martani mai tsauri tare da zargin Houthi da raunata akalla mutane 73 a hare-haren.

Rikici ya kara kamari a Yemen

Kara karanta wannan

Rigima sabuwa: Jiragen yaki sun yi barin wuta a Saudiyya, an tafka asara

Rikicin tsakanin kungiyar Houthi da Saudiya na ci gaba ne a yayin da kungiyar ke yaki da gwamnatin Yemen da Riyadh ke goyon baya kuma kasashen duniya suka amince da ita.

Gwamnatin Yemen ta sanar ranar Litinin cewa ta kaddamar da farmakin martani kan yankunan da Houthi ke rike da su a wasu larduna daban-daban.

Hari.
Makami mai linzami da mayakan Houtsi suka harba a rikicin da ke faruwa a Yemen Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sabon tashin hankalin ya zama mafi tsanani tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da manyan fada a shekarar 2022.

Kafin yarjejeniyar, rikicin ya shafe shekaru takwas yana ci gaba, inda aka kashe dubban mutane a daya daga cikin kasashen da suka fi fama da talauci a duniya.

Saudiyya ta gayyaci Iran hadakar tsaro

Kun ji cewa Iran ta samu gayyata domin shiga sabuwar yarjejeniyar tsaro ta Makkah da Saudiyya, Turkiyya da Pakistan suka kafa a watan Agustam da ya gabata.

Wani babban jami'in Iran ya ce gwamnati na nazarin gayyatar, yayin da har yanzu kasashen da ke cikin yarjejeniyar ba su tabbatar da batun a hukumance ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262