Abubuwa Sun Birkice wa Netanyahu da Sabuwar Matsala Ta Tunkaro Shi a Israila
- ’Yan adawar Isra’ila sun nemi Benjamin Netanyahu ya bar mulki bayan rahoton cewa shugaban UAE ya gargade shi kan shirin Hamas kafin harin 7 ga Oktoba
- Gadi Eisenkot ya zargi Netanyahu da yin watsi da gargadin tsaro da dama, yayin da Naftali Bennett ya ce yana da alhakin kisan da aka yi
- Ofishin Netanyahu ya musanta rahoton Haaretz, yana mai cewa labarin ƙarya ce tsantsa tare da musanta cewa firaministan ya tattauna da shugaban UAE
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv, Israila - Manyan ’yan adawar siyasar Isra’ila sun ce Firaminista Benjamin Netanyahu bai cancanci ci gaba da riƙe mukaminsa ba.
'Yan adawan sun bayyana hakan ne bayan wani rahoto da ya ce Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta gargadi Netanyahu kafin harin Hamas na 7 ga Oktoba, 2023.

Source: Twitter
Jaridar Haaretz ta ruwaito cewa Shugaban UAE, Mohamed bin Zayed Al Nahyan, ya tattauna da Netanyahu kusan mako ɗaya da rabi kafin harin.
A cewar rahoton, shugaban UAE ya sanar da Netanyahu cewa Hamas na shirin wani babban farmaki.
Ofishin Netanyahu ya musanta rahoton
Ofishin Netanyahu ya musanta rahoton, yana mai bayyana shi a matsayin “ƙarya tsantsa.”
Ofishin firaministan ya kuma musanta cewa Netanyahu ya yi wata tattaunawa da shugaban UAE a lokacin da ake magana a kai.
Sai dai rahoton jaridar ya ƙara tayar da muhawara kan gazawar hukumomin tsaron Isra’ila wajen hana harin Hamas.
Eisenkot ya ce Netanyahu bai cancanta ba
Gadi Eisenkot, tsohon kwamandan sojin Isra’ila kuma ɗaya daga cikin manyan abokan hamayyar Netanyahu a zaɓen da za a gudanar ranar 27 ga Oktoba, ya zargi firaministan da gujewa ɗaukar alhakin gazawar tsaro.
Eisenkot a shafinsa na X ya ce Netanyahu ya samu gargadi da dama kafin harin, amma ya yi watsi da su.
“Netanyahu ya samu gargadi da dama game da 7 ga Oktoba kuma ya yi watsi da dukkansu. Bai cancanci ci gaba da mulki ba,” in ji Eisenkot.

Kara karanta wannan
Rashin tsaro: Janar Musa ya ce Najeriya ta yi galaba kan 'yan ta'adda, ya gabatar da dalili
Bennett ya zargi Netanyahu da alhakin kisan
Tsohon Firaminista Naftali Bennett, wanda shi ma ke neman kujerar firaminista a zaɓen, ya ce Netanyahu yana da alhakin abin da ya faru a ranar 7 ga Oktoba.
Bennett a wani rubutu a shafinsa na X ya ce Netanyahu yana da “alhakin kai tsaye da na kansa” kan mutuwar mutanen da aka kashe a harin, wanda ya zama mafi muni a tarihin Isra’ila.
“Netanyahu ba zai iya ci gaba da riƙe mukaminsa ko da na minti ɗaya ba,” in ji Bennett.
Shi ma Yair Golan, shugaban jam’iyyar Democrats, ya zargi Netanyahu da “jefa Isra’ila cikin haɗari.”
Ya ce bayanan cewa “babu wanda ya tashe ni” ba za su ƙara zama uzuri ba, yana mai cewa Netanyahu ya sani, ya yi watsi da gargadin kuma ya gaza.
Ana neman yin bincike mai zaman kansa
Shekaru bayan harin, Isra’ilawa da dama na ci gaba da neman kafa wani kwamiti mai zaman kansa domin gudanar da bincike kan gazawar tsaro da ta bai wa Hamas damar kai harin.
Jam’iyyun adawa sun ce kafa irin wannan kwamiti zai kasance babban abin da za su fara yi idan suka lashe zaɓe. Sai dai gwamnatin Netanyahu ta ƙi amincewa da buƙatar kafa kwamitin.
Rahoton ya ce Sinwar ya yi gargadi
Haaretz ta kuma ce tsohon shugaban Hamas, Yahya Sinwar, wanda Isra’ila ta kashe daga baya, ya sanar da wani tsohon jami’in Falasɗinawa cewa mayakan ƙungiyar na shirin wani “babban farmaki mai ban tsoro.”
An ce Sinwar ya kira shirin “girgizar ƙasa.” A cewar jaridar, tsohon jami’in Falasɗinawan ya isar da saƙon ga wani mai ba shugaban UAE shawara, wanda shi kuma ya kai saƙon ga shugaban UAE.
Daga nan ne aka ce shugaban UAE ya tuntubi Netanyahu domin sanar da shi abin da ake shiryawa.

Source: Getty Images
An mayar da yaron Netanyahu Israila
A wani labarin kuma, kun ji cewa an gaggauta mayar da Yair Netanyahu, babban ɗan Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, daga Amurka zuwa Isra’ila.
An mayar da babban yaron na Netanyahu zuwa Israila ne bayan hukumar leƙen asirin cikin gida ta ƙasar ta gano wata barazana ga rayuwarsa.
Asali: Legit.ng

