Ministan Tinubu Ya Fito Ya Fadi Gaskiya, Ya Ce Abin da Aka Yi Wa Peter Obi bai Dace ba
- Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce bai dace a hana Peter Obi zirga-zirga domin harkokin siyasa ba
- Wasu fusatattun matasa sun tare hanyar Makurdi zuwa Gboko tare da hana ayarin Obi wucewa zuwa Yelewata
- Keyamo ya ce ya kamata masu fushi da 'yan siyasa su bayyana matsayarsu ta hanyar kada kuri'a ba tashin hankali ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya shiga jerin masu Allah-wadai da tare hanyar dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, da wasu fusatattun matasa suka yi a jihar Benue.
Obi ya je jihar Benue ne domin harkokin siyasa gabanin zaben shugaban kasa na 2027, tare da shirin ziyartar Yelewata domin jajanta wa wadanda harin watan Yunin 2025 ya rutsa da su.

Source: Facebook
Abin da aka yi wa Peter Obi
Tashar Channels tv ta ce matsalar ta fara ne bayan ayarin Peter Obi ya yi karo da wani shingen hanya da fusatattun matasa suka yi.
An ce lamarin ya faru ne bayan ayarin ya yi nisa kadan daga filin jirgin sama a kan babbar hanyar gwamnatin tarayya ta Makurdi zuwa Gboko mai tituna biyu.
Matasa sun tare hanyar gaba daya, lamarin da ya haddasa cunkoson ababen hawa tare da hana sauran matafiya wucewa.
Keyamo ya ce bai dace ba
Da yake martani, Keyamo ya ce duk da bambancin ra'ayi kan dalilin zanga-zangar, bai dace a hana Obi ci gaba da tafiyarsa ba.
Ya ce ko zanga-zangar ta samo asali ne daga rikicin cikin gida a NDC, kamar yadda gwamnatin jihar Benue ta yi ikirari, ko kuma wata jam'iyyar siyasa ce ta dauki nauyin matasan, bai kamata irin wannan ya faru ba.
Keyamo ya kuma yi tsokaci kan masu zargin Obi da kokarin amfani da ziyarar Yelewata wajen tayar da hankalin jama'a domin dalilan siyasa.
A sakon da ya wallafa a X, Keyamo ya ce:
"Hakan ba amincewa ba ne. Ya kamata kowa ya samu damar zirga-zirga cikin yanci da gudanar da siyasarsa ba tare da irin wannan katsalandan mara kyau ba."
Ministan Tinubu ya caccaki yan jarida
Keyamo ya soki yadda kafafen yada labarai ke daukar labarai, inda ya ce lamarin ya sake nuna yadda wasu bangarorin kafafen yada labarai ke fassara abubuwan siyasa ta bangare guda.
A cewarsa, idan fusatattun mutane suka tare ko ci zarafin dan takarar jam'iyyar APC, wasu kafafen yada labarai kan bayyana lamarin a matsayin kin amincewar yan Najeriya.

Source: Facebook
Sai dai idan makamancin haka ya faru da dan takarar jam'iyyar adawa, sai a bayyana shi a matsayin hari daga yan daba ko wasu da aka dauki nauyinsu.
Keyamo ya ce ya kamata kafafen yada labarai su daina irin wannan son kai da fifita bangare guda tare da yi wa kowane bangare adalci.

Kara karanta wannan
Halin da ake ciki da yan sanda suka tabbatar da hari kan ayarin motocin Peter Obi
Kwankwaso ya yi tir da tare Peter Obi
Kun ji cewa Rabiu Kwankwaso ya yi Allah-wadai da tare ayarin Peter Obi a Benue, yana bayyana lamarin a matsayin barazana ga dimokuraɗiyya.
Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, ya bukaci gwamnatin Benue da ta tabbatar da tsaron Peter Obi da kuma sauran mutanen da ke cikin tawagarsa.
Ya kuma yi kira ga Shugaban Ƙasa da ya gargadi gwamnonin jihohi, musamman waɗanda ke cikin jam’iyyarsa, kan duk wani mataki da zai iya raunana dimokuraɗiyya.
Asali: Legit.ng

