'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Tsaro da Sace Kanin Dan Majalisa a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Tsaro da Sace Kanin Dan Majalisa a Kaduna

  • ’Yan bindiga sun kashe jami’an KADVS uku a hanyar Zaria zuwa Pambegua, bayan sun bi motar da ta ƙi tsayawa domin tantance mutanen da ke cikinta
  • Waɗanda aka kashe sun haɗa da Dallami Dantani, Abdullahi Hamisu da Zakariyya Musa, yayin da maharan suka tsere zuwa Zaria
  • Bayan harin, wasu ’yan bindiga sun shiga gidan ƙanin ɗan majalisar Kubau, Shehu Pambegua, inda suka sace Sunusi da misalin ƙarfe 10:00 na dare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Wasu 'yan bindiga sun kashe jami’an tsaro uku na 'yan sa-kan Kaduna State Vigilance Service (KADVS) a yankin hanyar Zaria-Pambegua da ke ƙaramar hukumar Kubau a Jihar Kaduna.

Mai magana da yawun KADVS, Yunusa Shehu Ibrahim, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 8 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi barna da suka farmaki gidan shugaban jam'iyyar ADC

'Yan bindiga sun yi barna a Kaduna
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Yadda aka kashe jami’an tsaron

Shehu Ibrahim ya ce lamarin ya faru ne ranar Litinin, 7 ga watan Satumban 2026 yayin da jami’an ke gudanar da aikin sintiri da duba tsaro na yau da kullum, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

A cewarsa, jami’an sun yi ƙoƙarin tsayar da wata mota kirar Volkswagen Golf mai launin ja, amma direban ya ƙi tsayawa.

Ya ce hakan ya sa jami’an suka bi motar da wata motar sintiri ta hukuma domin tantance mutanen da ke cikinta.

Sai dai Ibrahim ya ce daga baya mutanen da ke cikin motar sun buɗe wa jami’an wuta, inda suka kashe uku daga cikinsu.

Ya bayyana waɗanda aka kashe da sunayen Dallami Dantani, Abdullahi Hamisu da Zakariyya Musa.

Maharan sun koma ofishin KADVS

Mai magana da yawun KADVS ya ce bayan harin, ’yan bindigar sun juya zuwa wajen ofishin KADVS.

Ya ce maharan sun sake buɗe wuta, inda suka harbi Hamisu da Musa har suka samu munanan raunuka, kafin daga bisani su tsere zuwa hanyar Zaria.

Kara karanta wannan

Janar Christopher Musa ya kira ruwa, lauyoyin El Rufai sun nemi N10bn da wasu bukatu

An sace ƙanin ɗan majalisa

Sa’o’i kaɗan bayan harin, wasu ’yan bindiga sun kuma yi garkuwa da ƙanin ɗan majalisar dokokin Kaduna mai wakiltar mazabar Kubau, Shehu Pambegua.

Shehu Ibrahim ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare ranar Litinin a gidan ɗan majalisar da ke Pambegua, cikin ƙaramar hukumar Kubau.

A cewarsa, waɗanda ake zargin ’yan bindiga ne sun isa gidan ne a cikin wata mota kirar Sharon, inda suka shiga suka tafi da ƙanin ɗan majalisar mai suna Sunusi.

KADVS ta ƙara tsaro a yankin

Kwamandan kungiyar KADVS na Jihar Kaduna, Ali Audu, ya jajanta wa iyalan jami’an uku da aka kashe.

Ali Audu ya bayyana mutuwarsu a matsayin babban rashi mai raɗaɗi ga hukumar da kuma Jihar Kaduna baki ɗaya. Ya yaba da ƙarfin hali da jajircewar jami’an wajen gudanar da aikinsu, tare da tabbatar wa iyalansu cewa ba za a manta da sadaukarwar da suka yi ba.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa ya gano abin da ya hana a magance rashin tsaro a Najeriya

'Yan bindiga sun yi barna a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun hallaka​ mutane a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a wasu kauyuka da ke kananan hukumomin Giwa da Kubau na jihar Kaduna, i

Hatsabiban 'yan bindigan sun kashe mutane biyar tare da yin garkuwa da wasu 27 a yayin hare-haren ta'addancin da suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng