Manyan Labarai A Yau
NALPGAM ta yi gargadin cewa tashin farashin gas da ƙarancin kaya na iya haddasa matsalar ƙaranci tare da ƙara wa ‘yan Najeriya wahala. Farashin 1kg ya koma N2000.
'Yan daba sun ci karensu babu babbaka a wasu sassan jihar Kano. 'Yan daban sun kashe wasu mutane ciki har da wani sanda da ya kusa yin ritaya daga aiki.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wurin da ake gudanar da zaben fitar da gwani na jam'iyyar ADC. Sun yi awon gaba da jami'in hukumar INEC.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan tattaunawa domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Iran. Trump ya ce tattaunawa ta yi nisa.
Tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya shigar da korafi gaban 'yan sanda kan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Tsohon shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu Abubakar, ya yi barazanar raba gari da jam'iyyar APC biyo bayan zaben fitar da gwanin da aka gudanar.
Jami'an tsaron sirri na Amurka sun yi musayar wuta da wani mutum da ya yi harbi a kusa da fadar White House. Lamarin ya jawo an tsaurara matakan tsaro.
ADC ta sahalewa Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu Deen su kara a zaben fitar da dan takarar shugaban kasa da za a yi ranar Litinin.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya rubuta wasika ga hukumar PSC domin neman a yi wa wasu 'yan sanda karin girma na musamman.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari