Gwamnatin Tarayya Ta ba da Hutun Babbar Sallah, Ta Tura Sako ga Musulmin Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta ba da Hutun Babbar Sallah, Ta Tura Sako ga Musulmin Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta ba da hutun kwanaki biyu ga ma'aikata domin su samu damar gudanar da shagulgulan babbar Sallah ta bana 2026
  • Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Oji ya taya daukacin musulmi murnar zagayowar babbar sallah, daya daga cikin ibadun addinin musulunci
  • Gwamnatin tarayya ta kuma buƙaci ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a da nazari domin neman shiriyar Allah ga Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta ayyana ranaku biyu a matsayin hutun Babbar Sallah (Eid al-Adha) ta shekarar 2026.

Gwamnatin ta bayyana ranakun Laraba 27 ga Mayu da Alhamis 28 ga Mayu, 2026, a matsayin ranakun hutun ga ma'aikata domin bikin sallar layya watau Eid al-Adha na bana a Najeriya.

Kara karanta wannan

An kashe mutum 8 bayan dan majalisa ya bada kyautar miliyoyin Naira a jihar Neja

Tunji Ojo.
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo Hoto: @BTOofficial
Source: Twitter

An ba da hutun babbar sallah a Najeriya

Rahoton Vanguard ya ruwaito cewa Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar yau Litinin, 25 ga watan Mayu, 2027.

Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Magdalene Ajani, ce ta sanya wa hannu a jikin sanarwar a madadin Dr. Tunji Ojo.

Sanarwar ta ce gwamnatin Najeirya ta ba da wannan hutun domin nuna girmamawar ta ga addini da al’adun miliyoyin Musulman Najeriya da ke haɗuwa da sauran Musulmi a duniya wajen gudanar da wannan ibada.

Gwamnatin tarayya ta taya musulmi murna

Dr. Tunji-Ojo ya miƙa saƙon taya murna a madadin gwamnatin tarayya ga dukkan Musulmai a Najeriya da ma waɗanda ke ƙasashen waje.

Bugu da kari, ministan ya bayyana Babbar Sallah a matsayin biki mai matuƙar muhimmanci da ya samo asali daga sadaukarwa, biyayya ga Allah da kuma tausayi ga al’umma.

Kara karanta wannan

Albarkacin bikin babbar Sallah, gwamna zai fara rabon kayan abinci ga ma'aikata

Gwamnatin tarayya ta kuma buƙaci ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a da nazari domin neman shiriyar Allah ga ƙasa yayin da take ci gaba da ƙoƙarin samar da zaman lafiya, tsaro da ci gaba ga kowane ɗan ƙasa.

“Sakamakon 'yan uwanta, haɗin kai da kuma ƙaunar juna ne gwamnatin tarayya ke yi wa dukkan Musulmai fatan yin shagulgulan Babbar Sallah cikin kwanciyar hankali, albarka da farin ciki,” in ji sanarwar.

A ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, 2026, daidai da 10 ga watan Zul-Hijjah, 1446AH, musulmin Najeriya za su gudanar da babbar sallah ta bana.

A wani rahoton, kun ji cewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262