Trump Ya Yi Maganar Sulhu da Iran, Ya Fadi Makomar Mashigar Hormuz

Trump Ya Yi Maganar Sulhu da Iran, Ya Fadi Makomar Mashigar Hormuz

  • Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran domin kawo karshen yakin da ake yi
  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa tattaunawa ta yi nisa domin cimma yarjejeniya a tsakaninsu
  • Trump ya bayyana cewa mashigar Hormuz za ta kasance a bude nan ba da jimawa ba domin ci gaba da zirga-zirgar jiragen ruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi magana kan tattaunawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Trump ya bayyana cewa Amurka na ci gaba na tattaunawa da ƙasar Iran domin sake buɗe mashigar ruwa ta Hormuz.

Trump ya ce ana tattaunawa da Iran
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaba Donald Trump ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Asabar, 23 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

'Mutumina ne': Peter Obi ya yi magana da ake zargin yana gujewa Atiku

Ana takaddama tsakanin Amurka da Iran

Ikon mallakar wannan hanyar ruwa mai muhimmancin gaske ya kasance abin fafutuka tun lokacin da yaƙin da ya haɗa da Iran, Amurka, da kuma Isra'ila ya ɓalle a watan Fabrairu, inda ƙoƙarin diflomasiyya ya tsaya tsit na tsawon watanni.

A baya, Trump ya yi gargaɗin cewa mashigar za ta kasance "kulle cif-cif" har sai Iran ta amince da wata yarjejeniya da Amurka.

Katsewar zirga-zirga a wannan hanya ya hargitsa hanyoyin samar da man fetur na duniya, lamarin da ya sanya farashin danyen mai ya yi tashin gwauron zabi tare da tilasta wa ƙasashe da dama ɗaukar tsauraran matakan kiyaye amfani da makamashi.

Me Trump ya ce kan yarjejeniya da Iran?

Trump ya ce yanzu haka an "gama tattaunawa" kan yarjejeniyar tsakanin Amurka, Iran, da kuma ƙasashe da dama na ƙawance na Gabas Ta Tsakiya, inda a yanzu ake tattaunawa kan cikakkun bayanai na ƙarshe.

“Ina ofishin 'Oval Office' da ke Fadar White House inda muka kammala wata tattaunawa mai kyau sosai ta tarho da shugabannin ƙasashen Saudi Arabia, United Arab Emirates, Qatar, Pakistan, Türkiye, Egypt, Jordan, da kuma Bahrain game da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da dukkan abubuwan da suka shafi Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) mai nasaba da zaman lafiya."

Kara karanta wannan

Iran da Amurka: An samu sauyin farashin mai a duniya yayin da ake tattaunawar sulhu

“An riga an tattauna yarjejeniyar, sauran kammala ta tsakanin Amurka, Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da sauran Ƙasashe daban-daban.”

- Shugaba Donald Trump

Trump ya ce ana tattaunawa da Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Andrew Caballero-Reynolds
Source: Getty Images

Za a bude mashigar Hormuz

Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa ya yi magana daban da Benjamin Netanyahu, Firaministan Isra'ila, inda ya lura cewa tattaunawar ta tafi da kyau sosai.

“A halin yanzu ana tattaunawa kan fannoni da cikakkun bayanai na ƙarshe na yarjejeniyar, kuma za a sanar da su nan ba da jimawa ba."
“Baya ga sauran abubuwa da dama na yarjejeniyar, za a sake buɗe mashigar ruwa ta Hormuz.”

- Shugaba Donald Trump

An yi harbi a kusa da White House

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani mutumi ya yi harbi kan jami'an tsaro a kusa da fadar White House ta kasar Amurka.

Mutumin ya buɗe wuta a wani shingen binciken tsaro kusa da rukunin fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya yi sanadiyyar musayar wuta da jami’an tsaro.

Shugaba Donald Trump, wanda ke cikin fadar White House a lokacin da aka yi harbe-harben, bai samu kowane irin lahani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng