Rigima Ta Kunno Kai a Jam'iyyar APC, An Dakatar da Sanata Jibrin Isah
- Jam'iyyar APC a mazabar Odu ta dakatar da sanatan Kogi ta Gabas, Jibrin Isah wanda aka fi sani da Echocho bisa zargin cin amana
- Shugabannin APC na mazabar sun zargi sanatan da ganawa da jam'iyyun adawa, abin da suka ce ya saba wa kundin tsarin mulkin APC
- A nasa bangaren, Sanata Echocho ya yi fatali da dakatarwar yana mai cewa zarge-zargen da aka kakaba masa ba gaskiya ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kogi, Nigeria - Sanatan Kogi ta Gabas, Jibrin Isah, da shugabannin APC na Odu ta 2 a ƙaramar hukumar Dekina ta jihar Kogi sun fara ka-ce-na-ce kan dakatar da shi daga jam’iyyar.
A cikin wata sanarwa mai ɗauke da ranar 26 ga watan Mayu, 2026, wadda aka aika wa shugaban APC na jihar a Lokoja, shugabannin mazabar sun dakatar da Sanata Jibrin Isah, wanda aka fi sani da Echocho.

Kara karanta wannan
Mai dokar barci: Sojoji sun damke 'dan bijilanti da zargin yi wa ISWAP leken asiri

Source: Facebook
APC ta dakatar da sanata a Kogi
The Cable ta ruwaito cewa APC ta dakatar da sanatan ne bisa zarge-zargin da suka shafi cin mana da yi wa jam'iyya zagon kasa.
Shugabannin APC na mazabar Odu sun kuma yi zargin cewa sanatan ya kasa kawo nasara ga jam’iyyar a rumfar zaɓensa a zaɓukan gwamnan jihar Kogi na shekarun 2019 da 2023.
Dalilin dakatar da Sanata Jibrin
Sanarwar ta ce:
“Ya zo mana da takaici yadda Sanata mai wakiltar Kogi ta Gabas, Jibrin Isah (Echocho), ya daɗe yana aikata ayyukan adawa da jam’iyya."
“Sanatan ya kasa kawo nasara har a rumfar zaɓensa a zaɓukan gwamnan jihar Kogi na 2019 da 2023. Ya yi aiki da ya saɓa wa muradun jam’iyya a mazabarsa, ƙaramar hukumarsa da kuma yankin da yake wakilta.”
Shugabannin APC ɗin sun kuma zargi sanatan da gudanar da tarurruka da jam’iyyun adawa.
“Sanatan yana gudanar da jerin tarurruka da jam’iyyun adawa, abin da ya saɓa wa kundin tsarin APC kuma bai dace da matsayinsa a jam’iyyar ba,” in ji sanarwar.
“Saboda haka, APC ta mazabar Odu a ƙaramar hukumar Dekina ta jihar Kogi, bayan taron da ta yi a ranar 26 ga Mayu, 2027, ta amince da dakatar da Sanata Jibrin Isah (Echocho) daga APC,” in ji sanarwar.

Source: Getty Images
Sanata Echocho ya yi watsi da dakatarwar
Sai dai mai magana da yawun sanatan, Mikail Ibrahim, ya yi watsi da dakatarwar, yana mai cewa ba ta da tushe ko inganci.
A wata sanarwa da ya fitar domin mayar da martani, Ibrahim ya ce Sanata Echocho ya yi nasara a rumfar zaɓensa tare da bayar da gagarumar gudunmawa ga nasarar APC a zaɓukan 2019 da 2023.
A wani labarin, kun ji cewa
Asali: Legit.ng
