Yadda 'Yan Daba Suka Hallaka Dan Sanda da Wasu Mutane a Kano
- An samu asarar rayuka sakamakon fadam daba da aka yi tsakanin wasu kungiyoyi a.wurare daban-daban na jihar Kano
- Fadan ya jawo an hallaka wani jami'in dan sanda har lahira yayin da aka gab da cika lokacin da zai yi ritaya
- Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana kokarin da take yi domin ganin ta kawo karshen aikata miyagun laifuffuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Wani jami’in ɗan sanda da ke aiki a ofishin 'yaan sanda na Hotoro, wanda aka bayyana sunansa da Sani S.O, ya rasa ransa a lokacin wani fadan daba a Kano.
Jami'in dam sandan ya rasu ne lokacin wani fada da aka yi tsakanin ƙungiyoyin ’yan daba masu adawa da juna a Kano, saura watanni kaɗan ya yi ritaya.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe shi ne tare da wasu mutane huɗu a lokacin fadan a ƙarshen makon da ya gabata a yankin Hotoro da ke karamar hukumar Nasarawa.
Ana samun fadan daba a Kano
Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da aka ruwaito cewa an kashe mutane biyu a wani makamancin wannan fada tsakanin ’yan daba a Fagge da kuma maƙwabtan kasuwar mayankan shanu ta Kano.
Haka zalika, ranar Laraba, an ruwaito cewa ’yan daba sun kashe shugaban mahauta na karamar hukumar Tofa na jihar, Kaura Mamiyo, a lokacin wani taron siyasa na tabbatar da wani mamba na Majalisar dokoki ta jihar.
'Yan daban sun kashe shi ne ta hanyar amfani da gora/itace, bayan da suka yi ƙoƙarin amfani da wuƙaƙe da adduna amma hakan bai yi tasiri ba.
Yadda aka kashe dan sanda a fadan daba
Wata majiya na kusa da mamacin jami’an dan sandan ya bayyana cewa an tura shi ne tare da sauran abokan aikinsa domin tarwatsa ƙungiyoyin da ke faɗan, lokacin da ɗaya daga cikin ’yan daban ya harbe shi da bindigar farauta.
“Yana aiki ne a ofishin 'yan sanda na Hotoro kuma an tura shi tare da wasu domin tarwatsa ’yan daban. Ba tare da ya sani ba, ɗaya daga cikinsu yana ɗauke da bindigar farauta wadda suka yi amfani da ita suka harbe shi."
"An yi gaggawar kai shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa."
- Wata majiya
Me 'yan sanda suka ce?
Ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai yi nasara ba domin bai amsa kiran waya da saƙonnin tes ba har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto.
Sai dai, kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar ta ƙaddamar da sashen mayar da martani ga laifuffukan tashe-tashen hankula (VCRU) domin tunkarar laifukan tashe-tashen hankula cikin gaggawa da ƙwarewa.

Source: Original
Ya bayyana cewa sashen, wanda aka kafa a watan Afrilu na shekarar 2026 bisa umarnin shugaban rundunar ’yan sanda na kasa (IGP), an tsara shi ne domin mayar da martani cikin sauri ga kiran neman ɗauki, kariya daga laifuffukan tashe-tashen hankula, gami da tabbatar da ingantaccen bincike da gurfanar da masu laifi.
'Yan ta'adda sun hallaka 'yan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda dauke da makamai sun hallaka jami'an 'yan sanda a jihar Yobe.
Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami’ai 17 biyo bayan wani harin ta’addanci da aka kai a jihar Yobe.
'Yan ta'addan sun kai harin ne a makarantar runduna ta musamman ta sojojin Najeriya da ke Buni Yadi, a karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.
Asali: Legit.ng


