"Ku Yi wa Najeriya Addu'a" Ministan Tinubu Ya Aika Sakon Barka da Sallah

"Ku Yi wa Najeriya Addu'a" Ministan Tinubu Ya Aika Sakon Barka da Sallah

  • Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ya buƙaci ‘yan Najeriya su ƙara yawaita addu’o’in zaman lafiya da cigaban ƙasa yayin bikin Babbar Sallah
  • Idris ya ce darussan Eid-el-Kabir sun haɗa da imani, sadaukarwa, biyayya da haɗin kai kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya koyar
  • Ministan ya jaddada cewa gwamnatin Bola Tinubu na ci gaba da aiwatar da manufofin Renewed Hope domin gina Najeriya mai tsaro da wadata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa ƙasar nan addu’ar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaba yayin shagulgulan Babbar Sallah.

Ministan ya bayyana hakan ne cikin saƙon taya murnar Eid-el-Kabir da ya fitar ranar Laraba domin taya al’ummar Musulmi murnar bikin.

Kara karanta wannan

2026: Muhimman abubuwa da Tinubu Ya Fadawa 'Yan Najeriya a Sakon Barka da Sallah

Ministan yada labarai Mohammed Idris ya taya 'yan Najeriya murnar babbar Sallah
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Alhaji Mohammed Idris. Hoto: @HMMohammedIdris
Source: Twitter

Sakon barka da Sallah daga minista

Alhaji Mohammed Idris ya fitar da wannan sakon ne a shafinsa na X kamar yadda Legit Hausa ta gani.

A cewarsa, bikin babbar Sallah na ɗauke da manyan darussa na imani, biyayya, tausayi da sadaukarwa kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya nuna.

Mohammed Idris ya ce lokaci ne da ya dace ‘yan Najeriya su ƙarfafa haɗin kai, haƙuri da juna tare da rungumar kyawawan ɗabi’u da za su ƙara haɗa kan al’umma.

Ya ce:

“A madadin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya, ina miƙa gaisuwar taya murna ga dukkan al’ummar Musulmi a Najeriya da ma faɗin duniya baki ɗaya.”

Gwamnatin Tinubu na cigaba da aiki

Ya ƙara da cewa yayin da jama’a ke shagulgulan Sallah tare da iyalai da masoyansu, akwai buƙatar ci gaba da yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya da cigaba.

Ministan ya jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tana cigaba da aiwatar da manufofin Renewed Hope Agenda domin gina Najeriya mai tsaro, cigaba da wadata.

Kara karanta wannan

Goron Sallah: Gwamnan Kano ya gwangwaje ma'aikatan jiharsa da kyautar kudi

Haka kuma ya shawarci jama’a su yi amfani da lokacin Sallah wajen tallafa wa marasa galihu da ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna ba tare da la’akari da bambancin ƙabila ko addini ba.

Minista ya nemi Musulmi su yi wa Najeriya addu'a a lokacin bukukuwan Sallah.
Al'ummar Musulmi suna gudanar da sallar idi a Najeriya.
Source: UGC

An yi addu’ar albarka ga Najeriya

A ƙarshe, Idris ya yi addu’ar Allah Ya sa albarkar Sallah ta kawo zaman lafiya, farin ciki da yalwar arziki ga gidajen ‘yan Najeriya.

"Allah Ya sa albarkar wannan bikin Sallah ta kawo zaman lafiya, farin ciki, da yalwar arziki ga kowane gida, kuma Allah Ya karɓi addu’o’in mu da hadayar mu. Barka da Sallah."

- Alhaji Mohammed Idris.

Tinubu ya aika sakon barka da Sallah

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya al’ummar Musulmi a Najeriya da ma duniya baki ɗaya murnar Babbar Sallah.

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su rungumi sadaukarwa, haɗin kai da tausayi kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya koyar.

Tinubu ya ce bikin 'Eid-el-Kabir' na tuna wa mutane muhimmancin biyayya ga Allah da kuma sadaukarwa domin kyakkyawar manufa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com