Hukumar INEC Ta Daukaka Kara kan Soke Wani Bangaren Jadawalin Zaben 2027

Hukumar INEC Ta Daukaka Kara kan Soke Wani Bangaren Jadawalin Zaben 2027

  • Hukumar INEC ta daukaka kara kan hukuncin da ya soke duka wa'adin da ta sanya wa jam'iyyun siyasa a jadawalin babban zaben 2027
  • Lauyan INEC, Alex Izinyon (SAN), wanda ya shigar da kara a gaban kotun daukaka kara ta Abuja, ya nemi a jingine hukuncin da babbar kotun tarayya ta yi
  • A makon jiya ne, kotun tarayya ta soke wasu daga cikin tsare-tsaren INEC, ciki har da wa'adin zaben fitar da gwani da na mika sunayen 'yan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta daukaka kara kan hukuncin da ya soke wasu daga cikin tsare-tsaren da ta yi a jadawalin zaben 2027.

Hukumar INEC ta shigar da kara gaban Kotun Daukaka Kara, inda ta nuna adawa da hukuncin da ya soke wa'adin zaben fitar da gwani, mika sunayen yan takara da maye gurbin wasu gabanin zaben 2027.

Kara karanta wannan

"Kamar nadin sarauta," Masani ya yi kaca kaca a nasarar da Tinubu ya samu a APC

Amupitan.
Shugaban INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan yayin ganawa da kwamishinonin zabe a Abuja Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

INEC ta nemi a soke hukuncin kotu

Rahoton Leadership ya tatttaro cewa INEC ta roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja da ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya ta yanke a makon da ya gabata, wanda ya soke wani ɓangare na ƙa’idojin zaɓe da hukumar ta tanada.

A makon da ya gabata ne Mai Shari’a Muhammed Umar na Babbar Kotun Tarayya ya soke ƙa’idar da INEC ta fitar wadda ta umarci jam’iyyun siyasa su gabatar da rajistar mambobinsu kafin ranar 10 ga Mayu, 2026, a matsayin sharadin shiga zaɓen 2027.

Yadda aka soke tsarin INEC

Haka zalika, alkalin ya soke wa'adin zaben fitar da gwani, wa'adin mika sunayen 'yan takara da kuma wa'adin maye gurbin 'yan takara idan bukatar hakan ta taso.

Wata jam’iyyar siyasa mai suna Youth Party ce ta shigar da ƙara tana ƙalubalantar halaccin wannan tsare-tsaren da hukumar zaɓen ta yi gabanin zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2027: Atiku da manyan ADC za su san makomarsu game da takarar shugaban kasa

Kotun ta bayyana a hukuncinta cewa INEC ba ta da ikon rage wa’adin da Sashe na 29(1) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya tanada dangane da gabatar da bayanan ‘yan takara da rajistar mambobin jam’iyya.

Inec.
Tambarin hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Bukatar INEC a kotun daukaka kara

Sai dai a cikin takardar ɗaukaka ƙarar da aka rubuta ranar 25 ga Mayu, 2026, INEC ta hannun lauyanta, Alex Izinyon (SAN), ta roƙi kotun ɗaukaka ƙarar da ta soke hukuncin kotun ƙasa.

Baya ga neman a soke hukuncin, babban lauyan ya kuma buƙaci kotun ta dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an kammala sauraron ɗaukaka ƙarar, kamar yadda Daily Post ta kawo.

INEC ta karbi kundin mambobin jam'iyyu 22

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar INEC ta tabbatar da cewa jam'iyyun siyasa 22 sun mika kundin rijistar mambobinsu kamar yadda dokar zabe ta 2026 ta tanada.

Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kan Masu Zabe na.INEC, Mohammed Kudu Haruna, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rattaba wa hannu.

INEC ta ce mika kundin rajistar ya biyo bayan karin wa’adin da ta bai wa jam’iyyun siyasa bayan da suka nuna damuwa kan wa’adin farko a wani taro da aka gudanar ranar 24 ga Maris, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262