'Yan Bindiga Sun Sace Jami'in Hukumar INEC a wajen Zaben Fitar da Gwani
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wurin da ake gudanar da zaben fitar da gwani na jam'iyyar ADC a jihar Cross River
- Tsagerun 'yan bindigan sun yi awon gaba da wani jami'in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) yayin harin da suka kai
- Jami'an tsaro sun kai daukin gaggawa bayan samun labarin aika-aikar da 'yan bindigan suka yi a wajen zaben fitar da gwanin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Cross River - 'Yan bindiga sun sace wani jami'in hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a jihar Cross River.
'Yan bindigan sun sace jami'in ne bayan da suka hargitsa zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar ADC a karamar hukumar Yakurr ta jihar Cross River.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
'Yan bindiga sun sace jami'in INEC
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:15 na daren ranar 22 ga watan Mayu a otal ɗin 'Wummy Hotel' da ke yankin Ekori, inda aka gudanar da zaɓen fitar da gwanin na jam'iyyar.
A cewar rahoton, ƙungiyoyi biyu na mutanen da ake zargi masu garkuwa da mutane ne suka afka wa wurin a lokacin da ake gudanar da aikin zaɓen.
An rawaito cewa ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ta sace jami'in tattara sakamakon zaɓen na INEC, inda suka tursasa shi shiga cikin wata mota, kuma suka tilasta masa tura masu kuɗi har Naira 70,000 kafin su tsere daga wurin.
Sauran 'yan bindigan, wadanda suka zo a kan babur, sun kwashe akwatunan zaɓe daga wurin taron.
Sojoji sun kai daukin gaggawa
Biyo bayan rahotannin sirri kan lamarin, dakarun sojoji da ke aiki a karamar hukumar Yakurr sun yi wa waɗanda ake zargin kwanton bauna lokacin da suke ƙoƙarin tserewa, inda suka tare motar da ke ɗauke da jami'in da aka sace.
An samu nasarar ceto jami'in na INEC a lokacin gudanar da aikin, yayin da aka kama mutane uku da ake zargi.
Majiyoyin tsaro sun ce wani mutum daya da ake zargi ya tsere zuwa cikin wani daji dauke da bindiga, wayar salula, katin cirar kuɗi na ATM, jakar tafiya, da kuma wasu kayayyakin zaɓe.

Source: Original
Jami'in na INEC da aka ceto, 'yan bindigan da aka kama da kuma motar da aka kwato a halin yanzu suna tsare a hannun jami'an tsaron sojoji domin gudanar da bincike.
Jami'an tsaro sun ƙara ƙaimi ga ƙoƙarinsu na gano wanda ake zargin da ya tsere da kuma dawo da kayayyakin zaɓe da aka sace.
'Yan bindiga sun sace raguna
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wasu dillalan dabbobi ana shirin bikin sallah.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa mutane da suka fito daga jihar Kano sun gamu da maharan ne a kan hanyarsu ta zuwa Kogi.
Maharan sun sace raguna guda 11 yayin da ‘yan kasuwar ke hanyarsu ta zuwa Ankpa a Kogi domin kasuwanci.
Asali: Legit.ng

