White House: An Yi Harbe Harbe a Kusa da Fadar Shugaba Trump

White House: An Yi Harbe Harbe a Kusa da Fadar Shugaba Trump

  • Wani mutum ya zaro bindiga daga cikin jaka ya yi harbi kan jami'an tsaro a kusa da fadar White House ta kasar Amurka
  • Jami'an tsaro sun mayar da martani wanda hakan ya jawo aka yi musayar wuta wadda ta jawo asarar rai da raunata wani mutum
  • Hukumomi sun bayyana cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, yana cikin fadar White House lokacin da lamarin ya auku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - An tsaurara matakan tsaro a Fadar White House na ɗan lokaci a yammacin ranar Asabar, 23 ga watan Mayun 2026.

An tsaurara tsaron ne bayan wani mai ɗauke da makami ya buɗe wuta a wani shingen binciken tsaro kusa da rukunin fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya yi sanadin musayar wuta da jami’an tsaron sirri na Amurka.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram bayan musayar wuta a Borno

An kulle fadar White House ta Amurka
Jami'an tsaro na sintiri a fadar White House ta Amurka Hoto: Brendan Smialowski
Source: Getty Images

Jaridar Aljazeera ta ce lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan ƙarfe 6:00 na yamma a mahaɗar titin '17th Street' da 'Pennsylvania Avenue NW'.

An harbi jami'an tsaro a kusa da White House

Wanda ake zargin ya matso kusa da shingen bincike na jami'an tsaron sirrin, ya zaro makami daga cikin wata jaka, sannan ya fara harbin jami'an.

Jami'an tsaron sirrin sun mayar da martani da gaggawa ta hanyar buɗe wuta, inda suka raunata wanda ake zargin da munanan raunuka, wanda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa a wani asibiti na kusa.

Wani mai wucewa ta wajen shi ma ya samu rauni a lokacin harbe-harben, ko da yake jami'ai sun ce ba a tantance ko wane irin harsashi ba ne ya same shi ba. Ba a bayyana yanayin da mutumin yake ciki ba.

Manyan jami’an tsaro guda shida sun tantance sunan wanda ake zargin da Nasire Best.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Alkalin babbar kotun tarayya ta Kano, Mohammed Yunusa ya yi mutuwar fuju'a

A cewar manyan jami’an tsaro guda biyar, Best ya taɓa samun matsaloli na baya-bayan nan da jami’an tsaro na cikin gida, sannan yana da tarihin matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa.

Trump na cikin fadar White House

Shugaba Donald Trump, wanda ke cikin fadar White House a lokacin da aka yi harbe-harben, bai samu kowane irin lahani ba.

Hukumar tsaron sirrin ta kuma tabbatar da cewa babu wani jami’inta da ya samu rauni a lokacin lamarin.

Daga baya jami'ai sun yi wa Trump bayani kan halin da ake ciki dangane da harin da mutumin ya kawo.

An yi harbe harbe a kusa da fadar White House
Jami'an tsaro na kula da wani mutum da ya ji rauni bayan harbi a kusa da fadar White House Hoto: Roberto Schmidt
Source: Getty Images

An yi karin bayani

Yayin da take tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa, fadar White House ta wallafa a shafin X cewa:

“Jim kaɗan bayan ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Asabar, wani mutum a yankin titin '17th Street' da 'Pennsylvania Avenue' ya zaro makami daga jakarsa kuma ya fara harbi."
“’Yan sandan tsaron sirri sun mayar da martani da harbi inda suka samu wanda ake zargin, wanda aka kai shi wani asibiti a yankin inda aka tabbatar da mutuwarsa. A lokacin harbe-harben, wani mai wucewa ta wajen shi ma harsashi ya same shi."

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke tsohuwa mai taimakon 'yan ta'addan Boko Haram a Borno

“Babu wani jami’i da ya samu rauni. Shugaban ƙasa yana cikin fadar White House a lokacin da lamarin ya faru, sai dai babu wani mutum da ke ƙarƙashin kariyar hukumar ko kuma wani aiki da ya fuskanci cikas."
“Wannan lamari yana ci gaba da kasancewa ƙarƙashin bincike, kuma za a fitar da ƙarin bayanai da zaran sun samu.”

An kai hari a fadar White House

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani mutum ya kai hari a fadar White House lokacin liyafar shekara-shekara ta 'yan jarida.

Harin ya sa liyafar ta rikide zuwa tashin hankali bayan mutumin dauke da bindiga ya yi yunƙurin kutsawa cikin wurin taron da ke da tsauraran matakan tsaro.

Taron ya gudana ne a otal din Washington Hilton, inda manyan jami’an gwamnati da daruruwan ‘yan jarida suka hallara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng